Zaben Gwamnan Kogi: Hotuna Sun Bayyana Yayin da Buhari Ya Lamuncewa Ododo
- Dan takarar gwamnan jam'iyyar All Progressive Congress (APC) a jihar Kogi state, Usman Ododo, ya samu yardar shugaban kasa Muhammadu Buhari
- Gwamna Yahaya Bello ya gabatar da Ododo ga shugaban kasar a fadar Villa a ranar Juma'a, 28 ga watan Afrilu
- Shugaba Buhari ya bukaci Ododo da ya mayar da hankali kan batutuwa masu muhimmanci yayin yakin neman zabe
FCT Abuja - Gabannin zaben gwamna a jihar Kogi, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lamuncewa dan takarar jam'iyyar All Progressive Congress (APC), Usman Ododo.
Jaridar The Nation ta rahoto cewar gwamna mai ci, Yahaya Bello ne ya gabatar da Ododo a gaban Shugaban kasa Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Juma'a, 28 ga watan Afrilu.
Jim kadan bayan gabatar da shi, Ododo ya sanar da manema labarai na fadar shugaban kasa cewa ya yi niya kuma a shirye yake ya ci gaba daga inda Gwamna Bello ya tsaya a jihar Kogi idan ya lashe zaben.
Ododo ya bayyana cewa gogewarsa a fannin tattalin arziki a ma’aikatun gwamnati da masu zaman kansu yasa ya dace da jan ragamar shugabanci a jihar Kogi.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sai dai kuma, ya bayyana cewa yana da tabbacin cewa zai yi nasara a zaben gwamnan da za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamba.
Gwamna Yahaya Bello ya ba mazauna Kogi tabbacin ci gaba da Ododo
A daya bangaren, Gwamna Bello ya bukaci mutanen Kogi cewa shugabancin Ododo zai kai jihar ga matakin nasara domin za a ci gaba da ababen more rayuwa a jihar.
Ya ci gaba da cewar jam’iyyar APC reshen jihar Kogi tana nan a hade kuma ta shirya yin nasara zaben gwamnan.
An tattaro cewa yayin zantawa da Shugaba Buhari, an shawarci Ododo da ya bayar da hankali kan muhimman batutuwa yayin yakin neman zabe sannan ya tabbatar da ganin cewa jam’iyyar ta ci gaba da rike kujerarta a jihar, Vanguard ta rahoto.
Ododo ya zama dan takarar gwamnan APC a Kogi bayan kammala zaben fidda gwanin jam’iyyar a ranar Juma’a, 14 ga watan Afrilu sannan aka tabbatar da shi a wani taron jam’iyyar na musamman a ranar Asabar, 15 ga watan Afrilu.
Kwamitin karbar mulkin Kano ya zargi Ganduje da yi ma shirin mika mulki zagon kasa
A wani labari na daban, kwamitin karbar mulki na Abba Kabir Yusuf ya zargi Gwamna Abdullahi Ganduje da yi wa shirin mika mulkin jihar zagon kasa.
Asali: Legit.ng