Buhari Zai Zauna a Daura Na Wata 6 Sannan Ƴa Koma Kaduna Bayan Mika Mulki, Shehu
- Shugaba Muhammadu Buhari ya ce zai ɗauki watanni 6 a mahaifarsa Daura ta jihar Katsina bayan miƙa mulki a watan Mayu
- Buhari ya ce bayan shafe wannan lokacin a Daura, daga nan kuma zai koma Kaduna da zama
- Ya faɗi haka ne yayin ganawarsa da gwamnonin jam'iyyar APC karkashin jagorancin Gwamna Atiku Bagudu
Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ce zai zauna na tsawon watanni 6 a mahaifarsa Daura, jihar Katsina bayan miƙa mulki ga zababben shugaban ƙasa ranar 29 ga watan Mayu.
Buhari ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, ya fitar, jim kaɗan bayan shugaban ƙasan ya gana da gwamnonin APC ranar Alhamis.
A cewar Shugaba Muhammadu Buhari, bayan shafe watanni 6 a Daura, zai koma jihar Kaduna da zama, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Buhari ya gana da gwamnonin ci gaba
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa a ranar Alhamis, shugaba Buhari ya gana da ƙungiyar gwamnonin ci gaba (Gwamnonin jam'iyyar APC) a fadarsa Aso Rock, Abuja.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Gwamnonin APC karkashin jagoranci gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi sun ziyarci Buhari ne domin taya shi murnar nasarar da jam'iyya mai mulki ta samu a babban zaɓen 2023.
Idan baku manta ba, zaben shugaban ƙasa da mambobin majalisar tarayya ya gudana ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023, yayin da zaben gwamnoni da yan majalisar jihohi ya gudana ranar 18 ga watan Maris, 2023.
Buhari, wanda ya yi doguwar magana kan shirinsa bayan sauka daga mulki, ya ce ya yi niyyar zama a Daura na watanni 6 kafin daga bisani ya koma Kaduna.
Waɗanda suka halarci taron
Taron ya samu halartar gwamnonin jihohin Filato, Kaduna Jigawa, Imo, Kwara Ekiti, Nasarawa, Kuros Riba, Kogi, Legas, Katsina da Ogun.
Mataimakan gwamna daga jihohin Borno, Ebonyi, Gombe da kuma Kano sun wakilci iyayen gidansu a wurin taron.
A wani labarin kuma Jam'iyyar APC mai mulki ta yi karin haske kan labarin dake yawo game da raba muƙaman majalisa ta 10
Mai magana da yawun APC na ƙasa, Felix Morka, ya ce har yanzun jam'iyyar ba ta yanke shiyyar da zata baiwa shugabancin majalisar tarayya ba a zangon mulki na gaba.
Manyan masu neman shugabanci a majalisar sun fara kamun kafa tun bayan dawowar zababben shugaban kasa, Bola Tinubu.
Asali: Legit.ng