Har Yanzu Bamu Yanke Shiyyar da Zamu Ba Shugabancin Majalisa Ba, APC
- Jam'iyyar APC mai mulki ta musanta raba mukaman shugabancin majalisar tarayya ta 10 zuwa shiyyoyi
- Mai magana da yawun jam'iyar APC ta ƙasa, Felix Morka, ya ce jita-jitar da ake yaɗa wa ba gaskiya bace
- A wata sanarwa, APC ta ce zata fitar da bayanai a kafafenta sahihai idan ta cimma matsaya kan batun
Abuja - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta ce har yanzun ba ta yanke shiyyar da zata baiwa shugabancin majalisar tarayya ta 10 ba.
Channels tv ta rahoto cewa jam'iyyar ta faɗi haka ne a wata sanarwa da Sakataren watsa labarai na APC ta ƙasa, Barista Felix Morka, ya fitar.
Ya ce an ja halin jam'iyyar APC kan wani jadawalin raba muƙaman shugabanci majalisun tarayya zuwa shiyya-shiyya, wanda ke yawo a wasu kafafen sada zumunta.
Gaskiya Ta Bayyana Kan Dalilin Da Ya Sanya Shugaba Buhari Ya kasa Cika Wasu Alkawuran Da Ya Yi Wa 'Yan Najeriya
Amma a cewar gajeruwar sanarwan da kakakin jam'iyya mai mulki na ƙasa ya fitar, wannan jadawalin rarraba muƙaman da ke yawo ba daga APC ya fito ba kuma ya kamata mutane su yi watsi da shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Domin share tantama, har yanzu jam'iyya mai mulki ba ta yanke yadda zata rarraba muƙaman majalisa tarayya ta 10 ba," inji sanarwan, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
Daga ƙarshe, APC ta bayyana cewa da zaran ta ɗauki matsaya game da batun shugabancin majalisa zata sanar a sahihan kafafenta da aka sani.
Wannan jita-jita ta fara yawo bayan ganawar zababben shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da manyan masu ruwa da tsaki a APC da mambobin kwamitin ayyuka.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa manyan masu neman kujerar shugaban majlisar dattawa da kakakin majalisar wakilai sun kaiwa Tinubu ziyara a gidan da aka ware masa a Abuja.
Kowanensu na kokarin shigar da kudirinsa don samun goyon baya daga shugaban kasa mai jiran gado, amma har yanzun bai faɗi wanda yake so ba.
Ku Kara Hakuri Da APC Kan Raba Mukaman Majalisa Ta 10, Abdullahi Adamu
A wani labarin kuma Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Adamu, ya magantu kan shiyyar da APC zata kai mukaman majalisa
Adamu, ya gana da zababben shugaban ƙasa, Sanata Ahmad Lawan, da wasu manyan kusoshin jam'iyya mai mulki kan batun shugabancin majalisa ta 10.
Asali: Legit.ng