Buhari ya hadu da Gwamnoni a Aso Rock, Ya Nuna Masu Abin da Ya Taimaki Tinubu
- Gwamnonin Kebbi, Imo, Kwara, Ekiti, Kaduna, Kogi, Jigawa, da Katsinasun ziyarci Muhammadu Buhari
- Shugaban kasa mai barin gado ya ba Gwamnonin APC shawara, ya ce a dauki darasi daga faduwar PDP da LP
- A taron, an hangi Gwamnonin Legas, Kuros Ribas, Ogun da Nasarawa da wasu mataimakan Gwamnonin Jihohi
Abuja - Karfin hali da rashin dabara ne ya jawo ‘yan adawa su ka sha kashi a hannun jam’iyyar APC mai-ci, wannan shi ne ra’ayin Muhammadu Buhari.
A ranar Alhamis, The Nation ta fitar da labari cewa Mai girma Shugaban kasa ya yi zama da Gwamnoni da kuma wasu shugabannin jam’iyyarsa ta APC.
Shugaban na Najeriya mai barin gado ya yi kira ga APC ta yi hattara, ta guji irin wannan karfin hali, sannan ta dage domin ganin jam’iyyar ta rike mulki.
Shugaba Muhammadu Buhari ya soki jam’iyyun PDP da LP da dogara da wasu a kasashen waje domin samun nasara, a karshe Bola Tinubu ya lallasa su.
Gwamnoni sun hadu da Buhari
Yayin da Gwamnonin APC suka kai masa ziyara a fadar Aso Villa, Shugaban kasar ya ce har PDP da LP sun fara fadawa kasashen ketare za su kifar da APC.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Rahoton ya ce Buhari ya nuna yadda jam’iyya mai-mulki tayi ta-ka-tsan-tsan tare da sa ran samun nasara, sannan ta dage wajen kamfe har aka samu nasara.
"A yanzu sun gagara gamsar da wadanda suka mara masu baya a waje game da yadda suka gagara doke mu.
Wani muhimmin dalili da ya sa na ke taya Asiwaju murnar samun nasara shi ne ‘Yan adawa sun sa rai daga waje, su na cewa za su doke mu, su ci zabe."
- Muhammadu Buhari
Ganin abin da ya faru da jam’iyyun hamayya, The Cable ta ce Buhari ya fadawa Gwamnonin APC su hada-kai, su kuma rika magance matsalolinsu a tare.
Shirin ritaya bayan mulki
A jawabinsa, Mai girma Buhari ya yi maganar yadda yake shirin komawa gidan idan ya sauka, ya ce zai zauna a Daura na watanni shida kafin ya tare a Kaduna.
Shugaban kasar ya godewa Nasir El-Rufai ganin yadda ya samar da abubuwan more rayuwa, haka zalika ya yabi Gwamnan jihar Kano da yin irin haka a mulkinsa.
Za a je kotu a APC
A rahoton da mu ka fitar, an samu labari Salihu Mohammed Lukman zai yi shari’a da APC, Abdullahi Adamu, Iyiola Omisore da hukumar INEC a kotu.
Mataimakin shugaban APC mai wakiltar Arewa maso yamma ya shigar da kara a kotun tarayya, ya ce an sabawa doka kuma an kira kiran taron NEC.
Asali: Legit.ng