Tinubu Ya Amince da Gayyar Gwamna Wike Ta Kaddamar da Wasu Ayyuka a Ribas

Tinubu Ya Amince da Gayyar Gwamna Wike Ta Kaddamar da Wasu Ayyuka a Ribas

  • Shugaban kasa mai jiran gado, Aaiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya amince zai ziyarci jihar Ribas domin kaddamar da ayyukan gwamna Wike
  • Wike, a wata wasika mai ɗauke da kwanan watan 8 ga watan Afrilu,ya gayyaci Bola Tinubu ya kaddamar ayyuka 2
  • Manyan 'yan siyasan biyu suna ɗasawa da juna tun lokacin kakar kamfe duk da ba 'yan jam'iyya ɗaya bane

Abuja - Zababben shugaban ƙasa, Alhaji Bola Ahmed Tinubu, ya amince da gayyatar da gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike, ya masa ta zuwa kaddamar wasu muhimmin ayyuka ranar Laraba.

Bola Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas, ya tabbatar da amincewa da gayyatar a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Tuwita ranar Alhamis, 27 ga watan Afrilu, 2023.

Tinubu da Wike.
Tinubu Ya Amince da Gayyar Gwamna Wike Ta Kaddamar da Wasu Ayyuka a Ribas Hoto: preselecng
Asali: Twitter

Gwamna Wike ya gayyaci shugaban ƙasa mai jiran gado zuwa jihar Ribas domin ya kadddamar da gadar Rumuola/Rumuokwuta da sabon ginin Kotun Majistire ranar 3 da 4 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Bayan Ganawa da Tinubu, Shugaban APC Ya Yi Magana Kan Wanda Za'a Baiwa Shugabancin Majalisa Ta 10

Sanarwan ta ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Shugaban ƙasa mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya amince da gayyatar da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya aiko masa domin kaddamar da wasu ayyuka ranar Laraba."
"A wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 8 ga watan Afrilu, 2023, Wike ya gayyaci zababben shugaban kasa zuwa Ribas domin ya kaddamar da gadar Rumuola/Rumuokwuta da sabon ginin Kotun majistire a ranakun 3 da 4 ga watan Mayu."

Duk da Tinubu da gwamna Wike suna cikin jam'iyyu daban-daban amma manyan yan siyasan biyu suna ɗasawa tun lokacin kakar babban zaɓen shugaban ƙasa.

Ana ganin Wike, mamban babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa PDP, ya taimaka wa Bola Tinubu, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar APC a zaben 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Tinubu ya samu nasara da kuri'u mafi rinjaye a sakamakon zaben shugaban ƙasa daga jihar Ribas, wanda ake zargin gwamna Wike ne ya taimaka masa.

Kara karanta wannan

Somin-tabi: Bidiyon lokacin da Tinubu da Shettima ke kaura zuwa gidan gwamnati

NEC ta dakatar da batun cire tallafin Man Fetur

A wani labarin kuma Gwamnatin Tarayya Ta Sauya Tunani Kan Shirin Cire Tallafin Man Fetur a Najeriya

Majalisar kula da tattalin arziƙi a Najeriya ta dakatar da batun cire tallafin man fetur a karshen gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Ministan kudi, kasafi da tsare-tsaren ƙasa, Zainab Ahmed, ta ce NEC ta aminta a dakatar da shirin amma zasu ci gaba da tattaunawa kan batun a sabuwar gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262