Atiku Ya Ziyarci Babban Jigon Jam'iyyar APC, Sanata Orji Kalu, Gaskiya Ta Bayyana
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya kaiwa Sanata Orji Kalu na APC ziyara kan rasuwar mai ɗakinsa, Ifeoma
- Atiku ya ayyana marigayya Ifeoma a matsayin mace ta gari mai taimakawa al'umma kana ya roki Kalu ya ƙara hakuri da rashinta
- Bayan gaisawa, Atiku da Sanata Kalu sun shiga wata ganawar sirri wacce ta shafe kusan mintuna 30
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ranar Laraba 26 ga watan Afrilu, 2023 ya ziyarci mai ladabtarwa na majalisar dattawa, Sanata Orji Kalu, kan mutuwar mai ɗakinsa, Ifeoma.
Atiku, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP a zaben 25 ga watan Fabrairu, 2023, ya bayyana haka a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook kuma Legit.ng Hausa ta gani.
Haka nan a rahoton ziyarar da ta tattaro, Daily Sun ta ce Atiku, wanda ya dira gidan Kalu da ke Abuja da misalin ƙarfe 3:30 na rana, ya yi jimamin wannan babban rashi.
Abinda Atiku ya faɗa wa Kalu
Yayin da yake wa tsohon gwamnan jihar Abiya ta'aziyya, Atiku ya roki Sanata Kalu ya ɗauki dangana domin marigayya ta yi rayuwa mai amfani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya ayyana marigayya Ifeoma a matsayin mace mai nagarta, wacce ta sadaukar da kanta wajen yi wa al'umma aiki a zamanin rayuwarta.
Sanata Kalu ya maida martani
Da yake maida martani, Sanata Kalu ya gode wa Atiku Abubakar wazirin Adamawa bisa ware lokaci ya kawo masa ziyara a wannan lokaci na jimami.
Legit.ng Hausa ta gano cewa uwar gidan Sanata Orji Kalu, Ifeoma ta rasu tana da shekaru 61 a duniya.
Haka zalika rahotanni sun tabbatar da cewa bayan musayar gaisuwa da ta'aziyya, Atiku da Kalu sun gana na tsawon mintuna 30 amma a sirrance.
Ku Kara Hakuri Da APC Kan Raba Mukaman Majalisa Ta 10, Abdullahi Adamu
A wani labarin kuma Bayan Ganawa da Tinubu, Shugaban APC Ya Yi Magana Kan Wanda Za'a Baiwa Shugabancin Majalisa Ta 10
Har yanzu dai jam'iyyar APC ba ta bayyana yadda zata raba muƙaman majalisar tarayya ta 10 zuwa yankunan ƙasar nan ba.
Amma bayan zama da zababben shugaban ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya bukaci 'yan Najeriya su ƙara hakuri da batun raba mukaman shugabancin majalisa.
Asali: Legit.ng