Attajirin Dan Kasuwa, Aliko Dangote, Ya Ziyarci Bola Tinubu a Abuja

Attajirin Dan Kasuwa, Aliko Dangote, Ya Ziyarci Bola Tinubu a Abuja

  • Attajirin ɗan kasuwan nan ɗan asalin jihar Kano, Aliko Ɗangote, ya ziyarci shugahan ƙasa mai jiran gado a Abuja
  • Tinubu ya karbi bakuncin Attajirin da ya fi kowa kuɗi a nahiyar Afurka tare da wasu manyan jiga-jigan APC mai mulki
  • Duk da Atiku da Peter Obi sun kai ƙara Kotu, ana tsammanin Tinubu zai karbi ƙasa ranar 29 ga watan Mayu, 2023

Abuja - Fitaccen Attajirin ɗan kasuwan nan, Alhaji Aliko Ɗangote, ya ziyarci zababben shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, gabanin ranar rantsarwa 29 ga watan Mayu, 2023.

Wannan na ƙunshe ne a wani rubutu da zababben shugaban kasa ya wallafa a shafinsa na Tuwita kuma Legit.ng Hausa ta ci karo da shi ranar Laraba, 26 ga watan Afrilu.

Dangote da Tinubu.
Hotunan ziyarar da Ɗangote ya kaiwa Tinubu Hoto: @PresElectngr
Asali: Twitter

Tinubu ya karbi bakuncin Dangote, Attajirin da ya fi kowane baƙar fata kuɗi a Nahiyar Afirka bisa rakiyar kakakin majalisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Tinubu Ya Sa Labule da Shugaban APC Na Kasa da Wasu Jiga-Jigai, Bayanai Sun Fito

Sauran waɗanda suka raka Ɗangote sun haɗa da gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, tsohon shugaban EFCC, Nuhu Ribaɗu, James Falake da Ibrahim Masari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shafin zababben shugaban ƙasa ya wallafa Hotunan ziyarar Ɗangote kana ya ce:

"Shugaban ƙasa mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya karbi bakuncin Alhaji Aliko Ɗangote, bisa rakiyar Femi Gabajabiamila, Nuhu Ribaɗo, James Falake, Ibrahim Masari da sauransu."

Duk da yan adawa sun kalubalanci nasararsa a Kotu, ana tsammanin za'a rantsar da Tinubu ya karbi ragamar jagorancin Najeriya a ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

Tinubu ya gana da Tony Elumelu

Haka zalika a baya-bayan nan Tinubu ya gana da shugaban kamfanin Heirs Holdings, Tony Elumelu, domin tattauna batun lalubo hanyoyin da za'a tallafa wa matasan Najeriya.

Mista Elumelu ya wallafa Hotunan ganawarsa da zababben shugaban ƙasan a shafinsa na dandalin sada zumunta watau Instagram.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Mai Neman Shugabancin Majalisar Wakilai Ya Shiga Kus-Kus Da Tinubu, Bayanai Sun Bayyana

Bola Tinubu Zai Kaddamar da Wasu Manyan Ayyuka a Jihar Ribas

A wani labarin kuma Gwamna Wike ya tabbatar da ranakun da zababben shugaban ƙasa zai kai ziyara jihar Ribas

Nyesom Wike, wanda ke takun saƙa da Atiku Abubakar a jam'iyyar PDP, ya ce ya gayyaci Tinubu tun lokacin da ya zo kamfe.

Daga cikin ayyukan da ake tsammanin Tinubu zai buɗe har da katafariyar gadar da babu kamarta a Patakwal, babban birnin jihar Ribas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262