An Tsinci Gawar Dan Gwamnan Jihar Enugu A Inuwar APGA Bayan Ya Bata

An Tsinci Gawar Dan Gwamnan Jihar Enugu A Inuwar APGA Bayan Ya Bata

  • An tsinci gawar ɗan takarar da ya nemi tikitin gwamna a inuwar APGA a zaben jihar Enugu, Dons Ude
  • Bayanai daga majiya mai kwari sun nuna cewa ɗan siyasan ya ɓata tun ranar Asabar, yanzu an gano shi matacce
  • Har yanzun hukumar yan sanda reshen Enugu ba ta ce komai ba game da lamarin a hukumance

Enugu - Tsohon ɗan takarar gwamna karkashin inuwar jam'iyyar APGA a zaben da aka kammala kwanan nan a jihar Enugu, Injiniya Dons Ude, ya mutu.

Rahoton The Nation ya tattaro cewa Mista Ude, wanda aka ayyana ɓacewarsa tun ranar Asabar ɗin da ta gabata, an gano gawarsa.

Dons Ude.
An Tsinci Gawar Dan Gwamnan Jihar Enugu A Inuwar APGA Bayan Ya Bata Hoto:Dons Ude
Asali: Twitter

Wata majiya mai kusanci da iyalan gidansa ta shaida wa jaridar cewa an gano ɗan takara matacce a yankin 9th-mile a jihar Enugu da ke kudu maso gabashin Najeriya.

Kara karanta wannan

Bayanai Sun Fito Daga Tsagin Atiku, Da Yuwuwar Ba Za'a Rantsar da Tinubu a Matsayin Shugaban Ƙasa Ba

Bugu da ƙari, rahotanni sun nuna cewa an gano motarsa wacce ya ɓata tare da ita. Amma har kawo yanzu rundunar 'yan sanda ba ta ce komai ba a hukumance.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda ɗan siyasan ya ɓata

Tun da fari, idan an kira wayar ɗan takarar da ya nemi tikitin gwamna a APGA, Mista Ude ba ya ɗaga wa, lamarin da ya haifar da fargaba a zuƙatan makusantansa.

Ude, wanda ya taba riƙe mukamin Sakataren jam'iyyar PDP sau ɗaya kafin daga bisani ya koma APGA, rashin ɗaga wayarsa ta jawo aka fara tunanin ko ya faɗa hannun masu garkuwa da mutane ne.

A cewar wata majiya, bayan halin da aka shiga na rashin sanin inda yake, sai aka tsinci wayar salulansa a jikin katangar Caji ofis din yan sanda da ke Ugui, lamarin da ya ƙara tabbatar da rayuwarsa na cikin haɗari.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamna: Jerin Sunayen Manyan 'Yan Takarar Da Za Su Fafata a Zaben Gwamnan Jihar Kogi

Daga baya aka sanar da matarsa, wacce ta dage da kiran layinsa ko Allah zai sa ya ɗaga. An ce ta kai rahoton duk abinda ke faruwa wurin yan sanda tun da farko.

Yayin da aka tuntubi jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sandan Enugu, don jin ƙarin bayani ba'a same shi har yanzu da muke haɗa wannan rahoton, Channels tv ta rahoto.

Yan Sanda Sun Gano Masu Shirin Kai Hari Majalisar Dokokin Filato

A wani labarin kuma An Gano Masu Shirya Tuggun Kai Mummunan Harin Kisa Majalisar Dokokin Jihar Arewa

Rundunar yan sandan jihar Filato ta sanar da cewa ta gano wani shirin kai hari zauren majalisar dokoki, kuma ta gargaɗi duk mai hannu a lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262