Mai Neman Shugabancin Majalisar Wakilai Ya Shiga Kus-Kus Da Tinubu, Bayanai Sun Bayyana
- Hon. Mukhtar Betara Aliyu ya sanya labule da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
- Muktar Betara yana daga cikin masu zawarcin kujerar shugabancin majalisar wakilai ta tarayya
- Betara ya sanya labule da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ne a ƙoƙarin sa na samun goyon bayan sa domin ya gaji Femi Gbajabiamila
Abuja - Ɗaya daga cikin na gaba-gaba wajen neman kujerar kakakin majalisar wakilai ta tarayya, Hon. Muktar Betera Aliyu, ya ziyarci zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu domin neman goyon bayan sa.
Ɗan majalisar wakilan mai wakiltar Biu/Bayo/Shani da Kwaya Kusar a majalisar wakilai, na ci gaba da neman samun goyon baya a muradin sa na zama kakakin majalisar wakilai ta tarayya ta 10, cewar rahoton Tribune.
Zaɓaɓɓun ƴan majalisa, tsofaffin ƴan majalisa da masu ruwa da tsaki na ta nuna goyon bayan su ga ɗan majalisar, wanda suka bayyana a matsayin mutumin mutane ne.
Bayanai Sun Fito Daga Tsagin Atiku, Da Yuwuwar Ba Za'a Rantsar da Tinubu a Matsayin Shugaban Ƙasa Ba
Neman goyon bayan zaɓaɓɓen shugaban ƙasar da Betara ya je, na daga cikin yaƙin neman ɗarewa kan kujerar da ya ke ta yi tun watanni uku da suka gabata, kafin zuwan ranar rantsar da sabuwar majalisar wakilai a watan Yuni.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cikin wani faifan bidiyo da ofishin watsa labarai na ɗan majalisar suka fitar, Tinubi da kansa ya riƙe hannun Betara ya yin da ya yi masa iso zuwa cikin ɗaki domin tattaunawa, cewar rahoton Vanguard
Ziyarar da hon. Betera ya kai ta neman goyon bayan wajen Tinubu, ya yi ta ne a sabon mazaunin zaɓaɓɓen shugaban ƙasar da ke a gidan tsaro na ƙasa a birnin tarayya Abuja, bayan Tinubu ya dawo daga Umrah.
Waɗanda aka nuna a cikin bidiyon tare da Betara sun haɗa da shugaban majalisar dattawa mai barin gado, Sanata Ahmad Lawan, tsohon gwamnan jihar Ekiti, Dr. Kayode Fayemi da kuma sauran wasu na kusa da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar.
Amsar Mulki: Bayan Kwashe Kwanaki a Kasar Waje, Daga Karshe An Bayyana Ranar Da Bola Tinubu Zai Dawo Najeriya
Jakadan Najeriya Ya Fadi Gaskiyar Alakar Tinubu da Kasar Guinea
A wani rahoton na daban kuma, wani jakadan Najeriya ya bayyana gaskiya dangane da raɗe-raɗen da ake cewa Tinubu yana da fasfo na ƙasar Guinea.
An yi yada maganganu cewa Bola Tinubu yana da ƴancin zama ɗan ƙasa ƙasar Guinea, wanda hakan ba ƙaramin cece-kuce ya janyo ba a ƙasar nan.
Asali: Legit.ng