Zaben 2023: 'Yan Takarar Jam'iyyun ADC Da PDP Sun Maka Gwamnan Gombe a Gaban Kotu
- Ƴan takarar jam'iyyun PDP da ADC a zaɓen gwamnan jihar Gombe, ba su haƙura da.kashin da suka sha ba a zaɓen
- Ƴan takarar biyu sun garzaya gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓen jihar domin ƙalubalatar nasarar Inuwa Yahaya
- Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen jihar, za ta fara zama domin sauraron ƙararrakin a sati mai zuwa
Jihar Gombe - Ƴan takarar zaɓen gwamnan jihar Gombe, na jam'iyyun Peoples Democratic Party (PDP) da African Democratic Congress (ADC), Jibrin Barde da Nafi’u Bala, sun maka gwamnan jihar, Muhammad Inuwa Yahaya, a gaban kotun sauraren ƙararrakin zaɓe.
Jaridar Punch ta tattaro cewa Barde da Bala sun garzaya gaban kotun bayan bayyanar sakamakon zaɓen gwamnan jihar na shekarar 2023.
A takardar ƙarar da Barde ya shigar a gaban kotun, waɗanda aka sanya a cikin ƙarar sun haɗa da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), Inuwa Yahaya da jam'iyyar sa ta All Progressives Congress (APC), cewar rahoton Headtopics.
Kuma Dai: An Shigar Da Wata Sabuwar Karar Neman a Hana Rantsar Da Tinubu a Matsayin Magajin Shugaba Buhari
Wani ɓangare na ƙarar na cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Mai shigar da ƙara na farko, Jibrin Muhammad Barde, wanda ya yi zaɓe ya ke da ƴancin yin zaɓe sannan a zaɓe sa, ɗan takara ne a zaɓen gwamnan jihar Gombe, wanda aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris na shekarar 2023."
"Mai shigar na ƙara na farko ya yi takara a zaɓen a ƙarƙashin jam'iyya sannan mai shigar da ƙara na biyu ya ɗauki nauyin sa, sannan ya ce yana da ƴancin a ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen."
"Mai shigar da ƙara na biyu, jam'iyyar PDP, jam'iyyar siyasa ce mai rajista a Najeriya wacce ta ɗauki nauyin mai shigar da ƙara na farko ya yi takara a zaɓen gwamnan jihar Gombe wanda aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris 2023."
Za a fara sauraron ƙarar
Wani majiya a kotun wanda ya nemi a sakaya sunan sa, ya bayyana cewa a ranar Talata mai zuwa kotun za ta fara zaman ta.
"Za mu fara zaman mu na farko a ranar 2 ga watan Mayun 2023, da misalin ƙarfe 9 na safe. Idan kuka zo za ku ga yadda zaman zai kaya." A cewarsa.
Hukumar EFCC Za Ta Sake Maka Tsohon Minista a Gaban Kotu
A wani labarin na daban kuma, hukumar EFCC za ta sake gurfanar da tsohon ministan sufuri, Femi Fani-Kayode a gaban kotu.
EFCC na tuhumar Fani-Kayode da tsohuwar ministan kuɗi, Nenadi Usman, da almundahana da dukiyar ƙasa wacce ta kai N4.6bn.
Asali: Legit.ng