LP: “Mambobinmu Da Aka Dakatar Suna Kulla-Kulla Don Dakatar Da Karar Obi Kan Tinubu”
- Jam'iyyar Labour Party ta ce ta gano wasu bara gurbi a cikin 'ya'yanta wadanda ke yi mata zagon kasa
- LP ta ce akwai wasu mambobin jam'iyyar da ke shirya makirci don hana ruwa gudu a karar da Peter Obi ya shigar kan Bola Tinubu
- Ta yi kira ga hukumar tsaron kaya na DSS da hukumar EFCC da su kama su tare da yi masu tambayoyi kafin su tayar da kasar
Jam'iyyar Labour Party ta koka kan kulla-kullan da wasu mambobi da shugabanta ke yi na dakatar da karar da jam'iyyar ta shigar a kan Bola Tinubu da jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
A cewar jaridar Tribune, kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa (PEPT) za ta fara sauraron shari'arta nan da yan kwanaki masu zuwa.
Bangaren da Lamidi Apapa ke jagoranta suna cin dunduniyar jam'iyya, LP
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 25 ga watan Afrilu, Fasto Obiora Ifoh, mukaddashin kakakin LP, ya yi zargin cewa bangaren jam'iyyar karkashin jagorancin Lamidi Apapa, mataimakin shugabanta na kasa da aka dakatar, sune suka kulla makircin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani bangare na sanarwar na cewa:
"Da safen nan ne aka tunakari tawagar lauyoyinmu da bayanin cewa wadannan mutanen sun ci gaba da makircinsu ta hanyar tuntubar dukkan kotunan zabe inda yan takararmu da dama suka shigar da kararrakinsu na zaben da ya taso daga babban zaben da aka gudanar kwanan nan.
“Tare da Lamidi Apapa wajen kawo cikas ga nasarar da jam’iyyar Labour za ta samu a kotunan zabe da kuma kawo cikas ga ci gaban dimokuradiyya akwai wasu mambobin da aka dakatar da suka hada da Samuel Akingbade, Gbenga Daramola, Anselem Eragbe da Abayomi Arabambi da sauransu.
Tinubu Ya Shiga Matsala Yayin da Aka Shigar Da Sabuwar Kara Kotu Kan Dalilin Da Zai Sa a Dakatar Da Rantsar Da Shi
“Ku tuna cewa shugabancin Labour Party na ta nutso a kogin makirci, cin amana, ha’inci da zagon kasa daga wadannan tsoffin jami’ai na jam’iyyar."
Jam'iyyar ta kuma yi kira ga hukumar DSS da EFCC da su gaggauta kamawa da yi wa wadannan bara gurbi tambayoyi kafin su yi nasarar tayar da kasar, rahoton Vanguard.
Zuwa yanzu, bangaren jam'iyyar da Apapa ke jagoranta basu yi martani ga ikirarin ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.
APC ta fatattaki jiga-jiganta a jihar Edo
A wani labarin, jam'iyyar APC reshen jihar Edo ta kori mataimakin shugabanta da wasu mambobin jam'iyyar bakwai saboda zargin cin dunduniyar jam'iyyar.
Asali: Legit.ng