Wata Sabuwa: Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Nemi Kotu Ta Dakatar Da Rantsar Da Tinubu
- Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar HDP a 2019, Ambrose Owuru, ya shigar da sabuwar kara kotu kan bikin rantsar da Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa na gaba
- Owuwu ya nemi korun daukaka kara da ta dakatar da bikin rantsar da Bola Tinubu, yana mai zargin cewa shine ya lashe zaben shugaban kasa na 2019 kuma bai ci wa'adinsa ba
- Lauyan ya hada shugaban kasa Muhammadu Buhari, Abubakar Malami da hukumar zabe a matsayin wadanda ake kara na 1 zuwa na 3
Abuja - An tunkari zababben shugaban kasa, Bola Tinubu da sabuwar matsala gabannin rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu yayin da aka shigar da sabuwar kara kotun daukaka kara na Abuja don hana mika masa mulki.
Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Hope Democratic Party (HDP) a zaben 2019 kuma lauyan kundin tsarin mulki, Ambrose Owuru, ya shigar da karar mai lamba CA/CV/259/2023, jaridar Punch ta rahoto.
Mai karar ya sanya shugaban kasa Muhammadu Buhari, Abubakar Malami, Atoni Janar na tarayya kuma ministan shari'a, da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) a matsayin wadanda ake kara na 1, 2 da 3.
Tsohon dan takarar shugaban kasa na so a dakatar da bikin rantsar da Tinubu
Lauyan ya bukaci kotu da ta dakatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari, AGF da INEC gudanar da bikin rantsar da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu na ranar 29 ga watan Mayu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya yi ikirarin cewa shine ya lashe zaben shugaban kasa na 2019 kuma bai ci wa'adinsa na shekaru 4 ba.
Owuru, a kararsa, ya dage cewa Shugaba Buhari na ta amfani da wa'adinsa a mulki ba bisa ka'ida ba tun 2019 saboda kotun koli ta ki yanke hukunci kan karar da ya shigar a 2019, inda ya kalubalanci ayyana Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben.
29 Ga Watan Mayu: Fitattun Yan Najeriya 5 Da Ake Ganin Su Buhari Ke Baiwa Hakuri a Sakonsa Na Barka Da Sallah
Ya marawa kararsa baya da waa takardar rantsuwa mai layi 8, yana mai bukatar kotu da ta gaggauta sauraron karar kafin a iya rantsar da Tinubu.
Buhari ya ziyarci kasashe 43 a matsayin shugaban kasar Najeriya
A wani labarin, mun ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci kasashe 43 a tsawon shekaru takwas da ya shafe kan karagar mulki a matsayin shugaban kasar Najeriya.
Asali: Legit.ng