Rigima Ta Buɗe Sabon Shafi, An Dakatarda Shugaban PDP da Mataimakinsa a Legas
- PDP reshen jihar Legas ta dakatar da shugaban jam'iyya, Phillips Aivoji, da mataimakinsa, Benedict Felix Tai kan zargin cin amana
- Kwamitin ayyuka na jiha ya tabbatar da wannan dakatarwa ranar Talata, ya ce an yi haka ne domin ba su damar maida hankali kan Kes din dake Kotu
- Kakakin PDP ya ce bayan haka sun kafa kwamitin ladabtarwa da zai gudanar da bincike kan wasu zarge-zarge da suka taso
Lagos - Jam'iyyar PDP reshen jihar Legas, ranar Talata 25 ga watan Afrilu, 2023, ta dakatar da shugaban jam'iyya na jiha, Phillips Aivoji, da mataimakinsa, Benedict Felix Tai.
Rahoton Tribune Online ya ce tun da farko shugabannin PDP na matakin gunduma sun dakatar da jiga-jigan biyu bisa zargin zagon ƙasa da cin amana makonni kaɗan da suka shuɗe.

Kara karanta wannan
Daga Dawowarsa, Masu Neman Shugabancin Majalisa Sun Fara Sintiri Zuwa Wajen Tinubu

Asali: UGC
Sai dai shugaban jam'iyyar a Legas da mataimakinsa sun ce ba su gamsu da matakin ba, inda suka garzaya suka kalubalanci dakatarwan a gaban Kotu.
Meyasa PDP ta dakatar da shugabanta na Legasda mataimakinsa?
Amma a taron da mambobin kwamitin gudanarwa na PDP ta jihar Legas suka gudanar ranar Talaka, sun yanke dakatar da shugaban jam'iyya da mataimakinsa domin su maida hankali kan Kes din Kotu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kwamitin ya bayyana cewa Mista Aivoji da Mista Tai ba zasu gurfana a gaban ƙwamitin ladabtarwa ba.
Mataimakin shugaban jam'iyya na shiyyar Sanatan Legas ta yamma, Sunday Olaifa, ne zai maye gurbin shugaban jam'iyyar har zuwa lokacin da Kotu zata yanke hukunci.
PDP ta kafa kwamitin bincike
Bugu da ƙari, kwamitin gudanarwan PDP na jihar Legas ya kafa kwamitin ladabtarwa na mutum 7 domin bincike kan zargin zagon ƙasa da ake wa wasu jiga-jigai da mambobi ranar zaɓen gwamna.
Hakeem Amode, jami'in hulɗa da jama'a na PDP a jihar Legas, ya tabbatar da wannan ci gaban a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai ranar Talata.
Ya ce kwamitin ayyuka na jiha ya ɗauki waɗan nan matakan ne domun ceto jam'iyyar PDP, kamar yadda Punch ta ruwaito.
A wani labarin kuma Hadimin Atiku Abubakar ya ce mai gidansa zai samu nasara a Kotun sauraren ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa
Hadimin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar ya ce har yanzun nasarar Tinubu na tangal-tangal. A cewarsa, mai gidansa Atiku ne ya lashe zaben shugaban kasa kuma suna da hujja. Ya faɗi mafi karancin hukuncin da Kotu zata yanke kan babban zaɓen 2023.
Asali: Legit.ng