Zulum Da Buni Ke Kan Gaba a Tseren Zama Shugaban Kungiyar Gwamnoni NGF

Zulum Da Buni Ke Kan Gaba a Tseren Zama Shugaban Kungiyar Gwamnoni NGF

Gwamnonin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) guda biyu daga shiyyar arewa maso gabas ne ake ganin suna sahun gaba a jerin masu neman zama shugaban ƙungiyar gwamnoni (NGF).

Jam'iyyar APC, wacce ta samar da gwamnoni mafi rinjaye a zangon mulki na gaba, ɗaya daga cikin gwamnoninta ne zai karɓi shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya.

Haka nan jam'iyyar PDP da ke take mata baya a yawan gwamnoni, ita zata samar da mataimakin shugaban NGF, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Buni da Zulum.
Hoton haɗaka tsakanin gwama Mala Buni na Yobe da Babagana Zulum na Borno Hoto: Mai Mala Buni, Professor Zulum
Asali: Facebook

Jerin gwamnonin APC da ke sahun gaba

Legit.ng Hausa ta tattaro muku gwamnonin guda biyu da ake kyautata zaton ɗayansu ka iya zama shugaban NGF a zangon mulki na gaba, ga su kamar haka;

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Zaben Gwamna: Jerin Sunayen Manyan 'Yan Takarar Da Za Su Fafata a Zaben Gwamnan Jihar Kogi

1. Mai Mala Buni na jihar Yobe

2. Farfesa Babagana Umaru Zulum na jihar Borno

Daga cikin zaben gwamnoni 28 da aka fafata a ranar 18 ga watan Maris, 2023, jam'iyyar APC ta lashe jihohi 16, PDP ta ci 10, Labour Party ta samu ɗaya yayin da NNPP ya lashe zaɓen gwamnan Kano.

Gwamnonin APC 7 da Suka samu nasarar zarcewa kan kujerunsu sun ƙunshi, Inuwa Yahaya (Gombe), Mai Mala Muni (Yobe), da Abdullahi Sule (Nasarawa).

Sauran sun haɗa da, Babajide Sanwo-Olu (Legas), Dapo Abiodun (Ogun), AbdulRahman AbdulRazaq (Kwara), da kuma Babagana Zulum (Borno).

Adadin da kowace jam'iyya ta samu a jihohi 36

Dauda Lawal Dare na jam'iyyar PDP ya kwace mulki daga hannun gwamna Bello Matawalle na jam'iyyar APC a Zamfara yayin da Abba Kabir Yusuf na NNPP ta ya kwace mulki a Kano.

A jumullar jihohi 36 da ke faɗin Najeriya, jam'iyyar APC na da gwamnoni 20, PDP na da 13, sai kuma jam'iyyun APGA, LP da NNPP kowanen su na da gwamna guda ɗaya.

Kara karanta wannan

Sunayen Tsofaffin Gwamnonin Jihohi Masu Lissafin Zama Shugaban Sanatoci a Bana

A al'ada, shugaban NGF na fitowa daga jam'iyya mai rainjayen gwamnoni kuma gwamnonin da suka hau kan karagar mulki a karon farko ba su da ikon neman muƙamin.

Haka zalika, ana tsarin karba-karba a kujerar shugaban gwamnoni tsakanin arewa da kudu kuma kudu ce ta samar da shugaban NGF na ƙarshe, Kayode Fayemi na Ekiti.

Bisa haka ana tsammanin sabon shugaban gwamnoni zai fito daga arewa. Wasu majiyoyi sun ce Zulum da Buni ke kan gaba a tseren hawa wannan muƙami.

A cewar majiyoyin gwamna Buni da takwaransa Zulum na kan gaba ne saboda suna samun goyon baya daga jam'iyyar APC da kuma takwarorinsu gwamnoni.

Na shirya ɗaukar nauyin Najeriya - Tinubu

A wani labarin kuma Daga Dawowa Gida, Tinubu Ya Faɗi Gaskiya Kan Rashin Lafiyarsa, Ya Aike da Saƙo Ga Yan Najeriya

Zababben shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya dawo gida Najeriya bayan shafe kusan wata ɗaya a ƙasar Turai.

Kara karanta wannan

Jerin 'Yan Takarar Gwamna Na APC, PDP da LP a Zaben Gwamna a Watan Nuwamba, 2023

Daga saukarsa a filin Nnamdi Azikwe, Bola Tinubu ya yi ƙarin haske kan jita-jitar rashin lafiya, ya ce ya shirya ɗaukar nauye-nauyen 'yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262