Bayan Kwanaki 33 a Kasar Waje, An Sanar da Lokacin da Bola Tinubu Zai Dawo Najeriya
- Akwai yiwuwar Bola Tinubu da Mai dakinsa, Sanata Remi Tinubu su dawo gida an jima
- Na hannun daman zababben Shugaban kasa, James Falake ya ce jirginsa zai sauka a yau
- Ana sa ran dawowar Shugaban mai jiran gado ya shawo kan yamutsin cikin Jam’iyyar APC
Abuja -Yayin da ake ta kai-komo kan wadanda za su zama shugabannin majalisa, rahotanni na nuna watakila Asiwaju Bola Tinubu ya shigo Najeriya.
Jaridar nan ta Punch ta ce akwai yiwuwar jirgin Asiwaju Bola Tinubu wanda shi ne shugaban kasa mai jiran gado, ya sauka a kasar nan a yau Litinin.
Dawowar zababben shugaban zai ba shi damar samun ta-cewa kan yadda siyasa take tafiya.
Hakan yana zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan majalisar gudanarwa watau NWC na jam’iyyar APC suke kokarin yin zama kan zaben majalisar tarayya.
29 Ga Watan Mayu: Fitattun Yan Najeriya 5 Da Ake Ganin Su Buhari Ke Baiwa Hakuri a Sakonsa Na Barka Da Sallah
Zaben shugabannin majalisa
Majalisar NWC za tayi kokarin gujewa abin da ya faru a 2015 da Bukola Saraki da Yakubu Dogara suka zama shugabanni ba don son jam’iyyar APC ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tun a watan Maris Bola Tinubu ya bar Najeriya zuwa Faransa da Ingila, har yanzu bai dawo ba, a wancan lokacin ya bar kasar ne domin ya samu hutu.
Jawabin James Faleke a Twitter
Sakataren kwamitin yakin neman zaben Shugaban kasa, James Faleke ya yi magana a shafin Twitter, yake cewa a ranar Litinin Tinubu zai dawo.
Hon. Faleke yake cewa jirgin ‘dan siyasar zai duro da karfe 2:00 tare da mai dakinsa, Remi Tinubu.
Masoya maza da mata na wannan tafiya ta musamman, ina mai sanar da ku cewa duk wanda yake garin Abuja ko Nasarawa...
...ana gayyatarsa wajen tarbo zababben shugaban kasa da Uwargidar Najeriya gobe (Yau) da karfe 2:00pm a sashen saukar shugaban kasa a babban filin tashin jirgin sama.
Lokacin sauka: Karfe 2 nr wurin haduwa: Ofishin kamfe; Lokacin tantancewa: Karfe 12 nr.
Za a bada motoci. Mutanen da aka tantance kurum za a bari su shiga filin tashi da saukar jirgin saman saboda hali na tsaro.
- Hon. James Faleke
Rahoton ya ce Faleke ya kuma tabbatar da NWC za ta zauna tun da kowa ya dawo daga Umrah.
Asali: Legit.ng