‘Yan Adawa Sun Fito Gaba da Gaba Domin Karbe Shugabancin Majalisa a Hannun APC
- Akwai zababbun majalisa da suke ganin za a iya yakar APC a zaben shugabannin majalisa
- ‘Yan majalisar da za a rantsar ba za su yarda su zama ‘yan kallo a takarar shekarar nan ba
- Wani ‘Dan jam’iyyar PDP yake cewa adadinsu ya sha gaban kason da ake bukata yau
Abuja - Wasu gungun zababbun ‘yan majalisar wakilan tarayya sun fito karara su na masu ayyana niyyarsu na neman shugabancin majalisa ta goma.
Rahoton Punch ya ce zababbun ‘yan majalisar sun yi wani taro a daren Juma’a a garin Abuja, su ka nuna za su shiga takarar da za ayi a shekarar nan.
‘Yan siyasar sun ce bayan an karasa ragowar zaben 2023, jam’iyyar APC ta rasa rinjayen da ta ke da shi, saboda haka ba dole su jagoranci majalisa ba.
Wani babban ‘dan jam’iyyar PDP a majalisar wakilan kasar, ya zanta da Punch a asirce, ya nuna cewa abubuwan ban mamaki za su faru a nan gaba.
'Yan adawa sun yi kwarin gwiwa
A karshen zaman na jiya, an tsaida matsaya cewa ganin dinbin adadin ‘yan adawa a majalisar wakilai, sun shirya neman kujerar shugaban majalisa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Bayan karashen zaben ranar Asabar, adadin ‘yan jam’iyyar hamayya ya tashi zuwa 182, kujera daya fiye da kason da ake nema wajen tsaida shugaba.
Zababbun ‘yan majalisar sun ce kundin tsarin mulkin 1999 ya ba kowane ‘dan majalisa damar tsayawa takarar shugaba, ba tare da duba jam’iyyarsa ba."
Bayanin bayan taro
Jawabin bayan taron ya nuna wadannan zababbun ‘yan adawa da za su je majalisar tarayya sun nuna ba za su goyi bayan ‘yan siyasa su yi amfani da su ba.
An fadi hakan ne ganin ana kokarin kebe kujerar shugabannin majalisa a wasu bangarori, suka ce menene ya hana a ware kujeru a babban zaben 2023.
Jam’iyyun hamayyar kasar nan da suka hada-kai su ne: PDP, LP, APGA, SDP, ADC da YPP.
Zaben da za ayi a bana
Labarin da muka samu a farkon makon nan ya nuna akwai yiwuwar Sanatocin Arewa irinsu Barau Jibrin ba za su kai labari a zaben 'Yan Majalisa ba.
Dalili kuwa shi ne Gwamnonin APC sun fi karkata ga 'Yan Kudu maso kudu ko Kudu maso gabas, irinsu Orji Uzor Kalu, Osita Izunaso da Godwill Akpabio.
Asali: Legit.ng