Gaskiyar Magana Ta Bayyana Kan Batun Hada Baki Da INEC a Yi Wa Binani Magudi a Adamawa
- Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta yi magana kan zargin da ake yi wa jami'an ta na shirya maguɗi a zaɓen gwamnan Adamawa
- Hukumar INEC tace sam wannan zargin ba ya da tushe ballantana makama inda ta nesan ta kanta da aikata hakan
- Hukumar zaɓen ta kuma yi kira ga al'umma da su toshe kunnuwan su kan wannan jita-jitar da ake yaɗa wa
Abuja - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta fito fili ta musanta zargin cewa wasu jami'an ta sun haɗa baki da gwamnatin jihar Adamawa domin yin maguɗi a zaɓen gwamnan jihar.
Jaridar Tribune ta kawo rahoto cewa, an yi zargin cewa wasu daga cikin jami'an hukumar INEC sun ziyarci fadar gwamnatin jihar cikin tsakar dare, domin kitsa yadda za a taimaka a yi wa gwamna mai ci Ahmadu Fintiri, maguɗi ya cinye zaɓen.
A wata da sanarwa kwamishinan INEC na ƙasa kuma shugaban kwamitin watsa labarai da wayar da kan masu kaɗa ƙuri'a, Festus Okoye, ya fitar a ranar Alhamis, ya ce ko kaɗan jami'an hukumar ba su ziyarci gidan gwamnatin ba kafin zaɓen cike gurbin gwamnan jihar na ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairun 2023.
"Domin kawar da wani dukkanin shakku, ba wani taro ko wata ziyara irin wannan da ta auku, ballantana kuma maganar jerin sunayen jami'an tattara sakamakon zaɓe. Irin wannan taron zai zama saɓawa rantsuwar kasancewa ƴan ba ruwan mu da mu ka yi ne." A cewarsa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Okoye ya yi nuni da cewa hukumar baturen zaɓe ɗaya kawai ta naɗa domin zaɓen gwamnan jihar, wanda kuma shine ya zama baturen zaɓen jihar na zaɓen shugaban ƙasa, cewar rahoton Punch
Okoye ya ƙara da cewa:
"Kamar sauran baturen zaɓe na ƙasar nan, shi ma hukumar INEC ta ba shi takardar aiki, kuma sai da aka sanar da kwamishinan zaɓen INEC na jihar."
"Haka kuma jerin sunayen jami'an tattara sakamakon zaɓen tuni aka tura shi zuwa jihar, inda shugaban INEC da kan shi ya sanya hannu a kowane shafi na jerin sunayen, tun kafin isar kwamishinonin INEC na ƙasa."
Festus Okoye ya kuma bayyana cewa babu wata ƙullalliya ta musamman da aka shirya domin jihar Adamawa, inda ya yi kira ga al'umma da su yi watsi da wannan jita-jitar.
Ba da Mace Nayi Takara ba – Fintiri ya Fadi Asalin Abokan Gwabzawarsa
A wani rahoton na daban kuma, gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya ce ko kaɗan ba da mace yayi takara ba a zaɓen gwamnan jihar da ya yi nasara.
Gwamnan ya bayyana sunayen mutanen da a cewarsa da su ya fafata a zaɓen gwamnan ba da Aisha Binani ta jami'iyyar APC ba.
Asali: Legit.ng