Zaben Adamawa: Zababben Shugaban kasa, Tinubu ya yi kira ga ‘Yan Sanda da Binani
- A matsayinsa na Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu ya fitar da jawabi a kan zabukan da aka yi
- Bola Tinubu ya ji dadi da yadda aka kammala zabuka cikin kwanciyar hankali a fadin Najeriya
- Amma Shugaban mai jiran gado yana so a binciki abubuwan da suka faru a zaben jihar Adamawa
Adamawa - Zababben shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya yi kira ga ‘yan sanda da su yi bincike a kan abin da ya faru a karashen zaben Gwamnan Adamawa.
A wani rahoto da ya fito a The Cable, an ji Asiwaju Bola Tinubu ya bukaci abin da ya kai-ya komo, kafin Hukumar INEC ta tabbatar da nasarar Ahmadu Fintiri.
Kafin a kai ga sanar da sakamakon zaben Gwmanan, Babban kwamishinan INEC, Hudu Yunusa-Ari ya yi katsalandan, ya ce Aisha ‘Binani’ Dahiru tayi nasara.
Kafin a je ko ina, hukumar INEC ta kasa ta rusa sanarwar jami’in, ta kuma dauki mataki.
Ayi cikakken bincike
A jawabin da ya fitar a ranar Laraba, Bola Tinubu ya bukaci jami’an tsaro su gudanar da bincike na musamman a kan ‘duk abubuwan da suka faru a zaben.'
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Zaben karashe da aka yi na 2023 ya zo karshe. Na lura da yadda akasari aka yi farin ciki da zabukan, kuma aka yi su cikin kwanciyar hankali a ranar Lahadi.
Hakan ya kara nuna mutanenmu sun runguma damukaradiyya, sun yi imani da tsarin zabenmu.
Amma na lura da abin da ya faru a karashen zaben Gwamnan Adamawa, kuma ina kira ga jami’an ‘yan sanda da suyi cikakken bincike kan duk abin da ya faru
Ganin irin ce-ce-ku-cen da aka samu. A duk wata gwabzawar damukaradiyya, dole bangare daya yake nasara. Ina kira ga wadanda ba su ji dadi ba, su bi doka.
Karfin hali: Matashi dan Arewa ya daura damara, zai yi tattaki daga jiharsu don shaida rantsar da Tinubu
- Bola Tinubu
Kira ga wadanda za su yi mulki
Duk da ba jam’iyyarsa tayi nasara ba, rahoto ya ce Bola Tinubu wanda ya tsaya takarar shugaban kasa a APC kuma ya yi galaba, ya taya wanda ya ci murna.
Zababben shugaban kasar ya bukaci wadanda suka lashe zaben su kara zage dantse wajen kokarin taimakawa talakawansu wajen ganin kawo cigaba a Najeriya.
Vanguard ta ce ‘dan siyasar ya yi amfani da damar wajen taya murna ga duk wadanda suka ci zabe.
Shugaban kasa mai jiran-gado ya yi kira da babbar murya a gare su da su hada-kai da shi wajen kawo gyara ta fuskar tsaro, tattalin arziki da cigaba a kasar nan.
Rikicin APC a Kogi
Ana da labari Sanata Smart Adeyemi ya ce Usman Ododo wanda ake cewa ya lashe zaben tsaida gwani a APC a Kogi, kakansu daya da Gwamna Yahaya Bello.
Daga baya an ji Gwamnatin jihar Kogi ta yi martani ga Smart Adeyemi, wanda ta ce Yahaya Bello ya ceto sa daga maraicin siyasa, amma ya ci amanar Gwamnan.
Asali: Legit.ng