Gwamna Fintiri Ya Karbi Shaidar Lashe Zaben Gwamna Daga Hannun INEC
- Gwamna Ahmadu Fintiri da mataimakiyarsa sun karbi shaidar lashe zaɓe daga hannun INEC ta ƙasa a Abuja
- Wannan na zuwa ne awanni bayan baturen zaben juhar Adamawa ya bayyana sakamakon zabe baki ɗaya
- Gwamnan Fintiri ya gode wa ɗaukacin mazauna Adamawa amma ya koka kan halin da REC ya nuna
Abuja - Zababben gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, da mataimakiyarsa, Farfesa Kaletapwa Farauta, sun karɓi Satifiket ɗin cin zaɓe a Abuja.
Hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta baiwa zababben gwamna da mataimakiyarsa shaidar lashe zaɓen Adamawa da misalin karfe 5:00 na yamma ranar Laraba.
Punch ta rahoto cewa baturen zaɓen jihar, Muhammed Melee, ya ayyana Fintiri na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓe a ranar Talata da ƙuri'u 430,861.
Gwamna Fintiri ya lallasa babbar abokiyar karawarsa, Sanata Aishatu Ɗahiru Binani, yar takarar gwamna a inuwar APC, wacce ta tashi da kuri'u 398,788.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Hukumar INEC ta sake buɗe zauren tattara sakamakon zaɓen da aka ƙarisa a jihar ranar Talata 18 ga watan Afrilu, 2023 kwanaki uku bayan kammala zaben.
Tun ranar Lahadi aka dakatar da tattara sakamako bayan kwamishinan zaben Adamawa (REC), Hudu Yunusa Ari, ya ayyana Aishatu Binani a matsayin wacce ta ci zaɓe.
Gwamna Fintiri ya yi jawabi
A rahoton The Cable, yayin da yake jawabinsa amincewa bayan lashe zaɓe, gwamna Ahmadu Fintiri ya ce, "An rage masa ƙima da yawa."
Yayin da yake taya abokan fafutukarsa bisa wannan nasara, Gwamna Ahmadu Fintiri, ya yi Alla-wadai da abinda Hudu ya yi, wanda ya ayyana Binani a matsayin gwamna.
A cewarsa abinda kwamiahinan zaɓen ya aikata, "ba'a yi tsammani ba," haka nan ya gode wa jama'ar jihar Adamawa bisa amince masa ya ɗora zuwa zango na biyu.
A wani labarin kuma Ana Fargabar Mutane Sun Mutu Yayin da Gini Ya Dane Ma'aikata a Abuja
Wani gini ya rufta kan jama'a a birnin tarayya Abuja, an rasa rayuka. Jami'an ba da agaji sun mamaye wurin don ceto waɗanda ginin ya rufe. Kawo yanzun an zaro mutum 4 da rai, wasu biyu kuma rai ya yi halins sanadin wannan aikin.
Asali: Legit.ng