Abin da Ya Hana Buhari Tsoma Baki a Tirka-Tirkar Binani da Fintiri – Gwamnatin Tarayya

Abin da Ya Hana Buhari Tsoma Baki a Tirka-Tirkar Binani da Fintiri – Gwamnatin Tarayya

  • Ministan yada labarai da al’adu na kasa ya yi magana game da zaben Gwamnan jihar Adamawa
  • An nemi jin abin da ya hana Shugaba Muhammadu Buhari cewa uffan yayin da aka samu rudani
  • Lai Mohammed yake cewa Shugaban kasa bai saba yi wa Hukumar INEC shiga sharo-babu shanu ba

Adamawa - A ranar Laraba aka ji Lai Mohammed yana bayanin abin da ya jawo shugaban kasa ya kauracewa hatsaniyar da aka shiga a jihar Adamawa.

Ministan yada labarai da al’adu bai tanka ba yayin da aka yi ta kai ruwa-rana a game da zaben Gwamnan Adamawa, Tribune ta kawo rahoton dalilin yin haka.

Alhaji Lai Mohammed ya ce hukuncin da za ayi wa Hudu Yunusa Ari ya ragewa hukumar zabe ta kasa watau INEC, wannan ba aikin shugaban kasa ba ne.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Bayan kammala zabe, an sace direban mataimakin gwaman Arewa

Lai yake cewa duk abin da Barista Hudu Yunusa Ari ya yi wajen ayyana ‘yar takarar APC a matsayin wanda tayi nasara a zabe, bai sa mai gidansa ya tanka ba.

Buhari bai yin shisshigi

Dalilin hakan kuwa shi ne, shugaban kasa bai yi wa hukumomin gwamnati kastalandan, yana barinsu su gudanar da harkokin gabansu yadda ya dace.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jaridar ta ce bayanan Ministan sun fito ne da yake zantawa da manema labarai bayan taron FEC da aka yi a fadar Aso Rock kamar yadda aka saba duk Laraba.

Adamawa
APC ta na kamfe a Adamawa Hoto: thenewshunterblog.wordpress.com
Asali: UGC

Ministan yana da labarin an aiko korafi zuwa ga Mai girma shugaban kasa domin ladabtar da Ari, sai ya ce jami’in ma’aikacin hukuma mai zaman kan ta ne.

Gwamnatin Buhari ba ta saba ba

Da aka matsa masa domin ya yi magana, Vanguard ta rahoto Lai yana cewa gwamnatinsu ba ta taba yi wa INEC katsalandan a kan ayyukanta ba.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Matashi dan Arewa ya daura damara, zai yi tattaki daga jiharsu don shaida rantsar da Tinubu

"Ba na tunanin gwamnatin nan ta taba tsoma baki a kan yadda hukumar INEC take shirya zabukanta.
Saboda haka babu dalilin gwamnati ta tsoma baki. Sha’anin INEC ne kuma hukumar ta dauki mataki a kai.
Shugaban INEC na yake kula da duka ma’aikatan INEC kuma yana daukar mataki. Me ku ke so a yi to?"

- Lai Mohammed

Duk da yadda aka nemi jin ta-bakin Ministan, sai ya nuna ba shi ya kamata a jefawa tambayar ba.

Za a biya Ifeanyi Ararume N5bn

A rahoton da mu ka fitar dazu, an ji Kotu ta dawo da tsohon Darekta mara iko da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kora daga Kamfanin NNPCL.

Ifeanyi Ararume bai wuce ‘yan kwanaki a ofis ba, aka sanar da shi cewa an fatattake shi daga mukaminsa. Hakan ya sa ya je kotu, kuma har ya yi nasara.

Kara karanta wannan

An Zarge Shi da Bada Cin Hanci, Dino Melaye Ya Fadi Yadda Ya Samu Takarar Gwamna

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng