Rikicin PDP: Patience Jonathan Ce Ta Taimakawa Wike Ya Zama Gwamnan Ribas, Dino Melaye

Rikicin PDP: Patience Jonathan Ce Ta Taimakawa Wike Ya Zama Gwamnan Ribas, Dino Melaye

  • Dino Melaye, dan takarar gwamnan PDP a zaben gwamnan jihar Kogi mai zuwa ya sake caccakar Gwamna Nyesom Wike
  • Melaye ya yi zargin cewa tsohuwar matar shugaban kasa Patience Jonathan ce ta dauki nauyin Nyesom Wike na jihar Ribas
  • A cewar tsohon dan majalisar, Wike ya ki la'akari da mutanen da suka taimake shi har ya kai sama yayin da yake alfahari game da wadanda shi ya taimaka

Rikicin da ke tsakanin Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas da Dino Melaye, dan takarar PDP a zaben gwamnan Kogi, ya dauki sabon salo.

Jaridar Tribune ta rahoto cewa, Melaye, a wata hira da Arise TV, ya yi zargin cewa Patience Jonathan, matar tsohon shugaban kasa ce ta dauki nauyin Wike ya zama gwamnan jihar Ribas.

Sanata Dino Melaye da Gwamna Nyesom Wike
Rikicin PDP: Patience Jonathan Ce Ta Taimakawa Wike Ya Zama Gwamnan Ribas, Dino Melaye Hoto: Nyesom Wike, Senator Dino Melaye
Asali: Facebook

Yadda Patience Jonathan ta dauki nauyin Nyesom Wike don ya zama gwamnan Ribas

Kara karanta wannan

Yadda Yahaya Bello Ya Kinkimo ‘Danuwansa, Ya ba Shi Takarar Gwamnan Kogi – Sanatan APC

Tsohon sanatan ya kara da cewar tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi da Peter Odili, sun ba da gagarumin gudunmawa a siyasar Wike, Premium Times ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan takarar gwamnan na Kogi ya zargi gwamnan Ribas da rashin godiya ga mutanen da suka taimaka masa har ya kai sama yayin da shi yake tunkaho game da mutanen da ya taimaka.

Melaye ya yi ikirarin cewa tsohon gwamna Odili ya nada Wike ya zama shugaban karamar hukumarsa. Ya kara da cewar Amaechi, tsohon ministan sufuri, ya nada gwamnan ya zama shugaban ma'aikatansa sannan ya zabe shi don zama ministan Najeriya.

Ya bayyana cewa tsohuwar matar shugaban kasar, Patience Jonathan, ta yi amfani da kudinta da hanyoyinta wajen tabbatar da ganin cewa Wike ya zama gwamnan jihar Ribas.

Tsohon dan majalisar tarayyar ya bayyana cewa da ba don kokarin tsohuwar matar shugaban kasar ba, da Wike bai zama gwamnan jihar Ribas ba.

Kara karanta wannan

Fintiri vs Binani: Gwamnan Adamawa ya yi bayani game da kitimurmurar zaben jihar

Wani bangare na jawabinsa na cewa:

"Misis Goodluck Jonathan ta kashe kudinta, hanyoyin da take da shi da komai don zamar da shi Gwamnan jihar Ribas."

Sau 19 Wike ya kirani yana so ya zama mataimakin Atiku, Dino Melaye

A baya mun ji cewa Sanata Dino Melaye ya bayyana cewa Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas na ta kamun kafa da shi a kokarinsa na son zama mataimakin Atiku Abubakar gabannin zaben shugaban kasa na 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng