Jerin Sanatocin PDP 6 Da Ka Iya Neman Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisa Ta 10

Jerin Sanatocin PDP 6 Da Ka Iya Neman Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisa Ta 10

Yayin da INEC ta kammala babban zaben 2023 bayan cikon da ya gudana ranar 15 ga watan Afrilu, 2023, a halin yanzun abin kallo ya koma majalisar tarayya ta 10.

Manyan zababbun Sanatoci a inuwar jam'iyya mai mulki watau APC sun fara rige-rigen neman muƙamai a majalisa ta 10 da za'a rantsar nan gaba.

Za'a iya cewa makamancin haka na fafutukar neman ɗarewa muƙamai masu gwaɓi ke faruwa a babbar jam'iyyar hamayya PDP.

Sanatocin PDP.
Jerin Sanatocin PDP 6 Da Ka Iya Neman Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisa Ta 10 Hoto: Aminu Tambuwal
Asali: Facebook

A wannan shafin, Legit.ng ta zaƙulo muku zababbun Sanatocin jam'iyyar PDP, waɗanda ake hasashen zasu iya neman kujerar shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa ta 10.

1. Seriake Dikson

Tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dikson, na ɗaya daga cikin jiga-jigan Sanatocin jam'iyyar PDP da suka samu nasarar lashe zaɓe a karo na biyu.

Kara karanta wannan

Rigima Sabuwa: Jam'iyyar APC Ta Kori Babban Sanata Mai Ci a Jihar Arewa, Ta Bayar Da Dalilai

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kafin hawa kujera lamba ɗaya a jihar Bayelsa da ke kudu maso kudancin Najeriya, Dikson ya rike kujerar mamban majalisar wakilan tarayya.

A yanzu yana ɗaya daga cikin manyan Sanatoci daga jam'iyyar adawa a majalisa. Ana tsammanin zai nemi muƙamin shugaban marasa rinjaye saboda gogewarsa a majalisa.

2. Abdul Ahmed Ningi

Ningi, tsohon mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, ɗan asalin jihar Bauchi ya dawo majalisar dattawa bayan goyon bayan da ya samu tsakanin 2011-2015, inda ya wakilci Bauchi ta tsakiya.

Ya riƙe kujerar shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan tarayya daga 2003 zuwa 2007. Babu tababa Ningi na cikin Sanatoci na sahun gaba da zasu nemi wannan muƙami.

3. Abba Moro

Tsohon ministan harkokin cikin gida, Abba Moro, ya samu nasarar komawa majalisar Dattawa a karo na biyu. Yana wakiltar mazaɓar Benuwai ta kudu.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Ta Doke Manyan Abokan Karawarta, Ta Lashe Ƙarin Kujerun Yan Majalisa 8

Duba da kusancinsa da tsohon shugaban majalisar dattawa kuma babban jigon PDP, David Mark, ana hasashen Moro zai nemi kujerar shugaban marasa rinjaye da taimakon uban gidansa a siyasa.

4. Adamu Alieru

Tsohon gwamnan Kebbi na ɗaya daga cikin jiga-jigan Sanatoci kuma na sahun gaba a jerim waɗanda ake ganin zasu iya ɗarewa muƙamin shugaban marasa rinjaye a majalisa ta 10.

Alieru ya rike kujerar ministan babban birnin tarayya Abuja lokacin mulkin marigayi Umaru Musa Yar'adua. Ya sauya sheka daga APC zuwa PDP ana dab da babban zaɓen 2023.

5. Jarigbe Agom Jarigbe

Ɗan shekara 52 a duniya, shi ne sanata mai wakilntar Kuros Riba ta arewa a majalisar Dattawa. Ya koma zango na biyu bayan turmushe gwamna Ben Ayade a zaɓen 2023.

Kafin ya tsoma ƙafa a majalisar dattawa, ya zauna a kujerar mamban majalisar wakilai. Ya shahara a jiharsa kuma sanannen mutum ne a tsakanin Sanatocin Najeriya.

Kara karanta wannan

Abu Ya Girma: Jam'iyyar APC Ta Dakatar da Ɗan Majalisar Tarayya Kan Babban Abu 1

6. Aminu Tambuwal

Tun dawowar mulkin Demukuradiyya a Najeriya ake damawa da Tambuwal a siyasa kuma ga dukkan alamau zai ci gaba da damawa.

Yayin da wasu ke ganin shi ne zai karbi kujerar shugaban marasa rinjaye, wasu na ganin gwamnan jihar Sakkwaton ka iya dafe kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawa.

Ya riƙe manyan muƙamai kamar mataimakin mai tsawatarwa a majalisar wakilai, shugaban marasa rinjaye, kakakin majalisar wakilai, gwamna tsawon zango biyu, shugaban gwamnonin PDP da shugaban NGF.

A wani labarin kuma Zababben Shugaban Kasa, Bola Tinubu Ya Bukaci Yan Sanda Su Binciki Rudanin Zaben Adamawa

A wata sanarwa da ya rattabawa hannu, Tinubu ya taya dukkan waɗanda suka ci zaɓe murna bayan kammala babban zaɓen 2023 ranar Asabar 15 ga watan Afrilu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262