Binani Ta Fede Gaskiyar Zargin Bada Naira Biliyan 2 Saboda Magudin Zama Gwamna
- Aishatu Dahiru (Binani) ta ce maganar bada cin hanci saboda ta iya lashe zabe ba gaskiya ba ne
- ‘Yar takararta APC a zaben Gwamnan Adamawa ta ce ana yi mata karyayyaki saboda adawa
- Sanata Binani ta kuma zargi Gwamnatin Ahmadu Umaru Fintiri da amfani da jami’an INEC
Adamawa - Aishatu Dahiru (Binani) ta musanya zargin da ake yi mata na bada cin hancin kudi saboda a sanar da ta zama zababbiyar Gwamnar Adamawa.
Tribune ta kawo rahoto cewa Sanata Aishatu Dahiru Binani ta karyata rade-radin da yake yawo na biyan cin hancin Naira biliyan 2 ga wasu ma’aikatan INEC.
‘Yar takarar ta tuhumi wani jami’in DSS da yi mata sharri mara makama da tushe, ta ce an yi hakan ne bayan da 'yan daban gwamna suka matsa masa lamba.
A jawabin da ta fitar a ranar Talata, Sanata Binani ta ce “BA TA TABA YI BA, kuma ba za tayi irin wannan danyen aiki ba, ta ce ita ba ta dauki abin da zafi ba.
Jawabin Aishatu Dahiru (Binani)
Ina so in jaddadawa mutane cewa nayi imani da damukaradiyya, ba zan taba yin abin da zai kawowa damukaradiyya cikas ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ban dauki lamarin siyasa a mutu ko ayi rai ba, a baya na lashe zaben majalisar wakilai da na majalisar dattawa ba da magudi ba.
"Abin da ya wakana a ranar Lahadi, yunkurin murde zaben jihar Adamawa ne a cewar ‘yar takarar.
- Aishatu Dahiru (Binani)
A cewar ‘yar takarar, abin da ya faru har jami’in REC ya fito yana bada sanarwa abin takaici ne, ta ce wasu Kwamishinoni ne suka nemi yi masa shisshigi.
An jefi jami'an INEC da rashin gaskiya
Har ila yau, Sanatar ta Adamawa ta tsakiya ta zargi wasu manyan jami’an INEC da zuwa gidan gwamnatin jihar Adamawa, sun hada-kai da gwamna mai-ci.
Punch ta ce Binani ta ce Gwamna mai-ci ne ya zabawa NEC wanda za su zama Turawan zabe.
"Ina kira ga masoyan damukaradiyya su sa kishin damukaradiyyarmu, ba a jihar Adamawa kadai ba, a duk fadin kasar.
Ga magoya baya na a gida da wajen Adamawa, ina so in yi amfani da wannan dama wajen gode maku yayin da ake fama da karya da furofagandar adawa."
- Aishatu Dahiru (Binani)
Taron dangi aka yi mani - Fintiri
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya fito yana cewa bai yi takara da wata mace a jihar Adamawa, an rahoto shi ya ce ya yi takara da makiyan damukaradiyya ne.
Kamar yadda Ahmadu Umaru Fintiri ya fada da aka zanta da shi, taron dangi aka yi masa, masu jin su ne suka mallaki Najeriya sun dage sai sun hana shi tazarce.
Asali: Legit.ng