Ba da Mace Nayi Takara ba – Fintiri ya Fadi Asalin Abokan Gwabzawarsa Bayan Ya Zarce
- Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya ce ba da mace ya gwabza wajen neman tazarce a 2023 ba
- Fintiri yana ganin was ‘Yan Siyasan Abuja ne abokan takararsa na ainihi ba Aisha Dahiru Binani ba
- Mai girma Gwamnan ya zargi wasu da ya kira makiyan jihar da kokarin hana shi komawa mulki
Adamawa - Zababben Gwamna kuma Mai-ci a jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya yi magana game da nasarar da ya samu a zaben da aka yi.
Da aka zanta da shi a filin siyasa na tashar talabijin Channels a ranar Talata, Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya ce rubdugu aka nemi yi masa.
Ahmadu Fintiri ya yi zargin cewa wasu manyan mutane daga Abuja ne suka dage kan cewa sai sun kakabawa mutanen jihar Adamawa sabon Gwamna.
Da yake bayani daga garin Yola ta kafar Zoom, Gwamnan ya ce ba da Aishatu Dahiru (Binani) ta jam’iyyar APC ya yi takara ba, taron dangi aka shirya.
"Ba da mace nayi takara ba"
Fintiri wanda ya samu kuri’u 430,861 a kan Binani mai 396,788, yake cewa babu wata mace da ya yi takara da ita, yana nufi ‘yar takarar APC mai mulki.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A rahoton Daily Trust, an ji Gwamnan yana cewa daukacin ma’aikatan hukumar zabe na kasa watau INEC, duk su na goyon bayan jam’iyyar APC ne.
“Ba na tunanin nayi takara da wata mace a jihar Adamawa, nayi takara da makiyan damukaradiyya ne daga wajen jihar Adamawa.
Taron dangi aka yi mani, nayi takara da wadanda suke Abuja, su na jin su ne suka mallaki Najeriya, sun dauki Adamawa kanwar lasa.
Ko a zaben, ban yi takara da mace ba, na gwabza ne da Hukumar INEC. Duka jami’an da ke aikin zaben nan, ‘ya ‘yan jam’iyyar APC ne.
- Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri
Ya aka yi PDP ta zarce?
Abin da ya taimake shi ya iya samun tazarce a cewarsa, shi ne aikin da ya yi wa Adamawa.
Idan har ba a dauki mataki a kan kwamacalar da ta faru a ranar Lahadi ba, rahoto ya zo cewa Gwamnan ya sha alwashin hukunta duk masu laifi.
Binani ta ruga kotu
A jiya ne aka ji labari Aisha Dahiru Ahmed Binani ta ce a dokar kasa, kotu kadai za ta iya soke zaben da aka lashe, don haka ta shigar da kara a kotu.
Idan da Sanata Aisha Dahiru Ahmed Binani ta yi nasara, kotu za ta bada umarni a dakatar da tattara zaben Jihar Adamawa bayan tirka-tirka.
Asali: Legit.ng