Kai Tsaye: An Cigaba Da Tattara Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar Adamawa

Kai Tsaye: An Cigaba Da Tattara Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar Adamawa

Jihar Adamawa - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta cigaba da tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar Adamawa. 

Jaridar Channels tv tace hakan na zuwa ne bayan an dakatar da tattara sakamakon zaɓen biyo bayan bayyana Aisha Dahiru Binani ta jam'iyyar APC, a matsayin wacce ta lashe zaɓen ana tsaka da tattara sakamakon zaɓen.

Tuni dai INEC tayi watsi da sanar da Binani a matsayin wacce ta lashe zaɓen, inda yanzu haka aka cigaba da tattara sakamakon zaɓen a cibiyar tattara sakamakon zaɓen gwamnan, da ke a Yola, babban birnin jihar.

Fintiri ya lashe zaben gwamnan Adamwa

A cewar hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), dan takarar PDP, Fintiri ne ya lashe zaben Adamawa da kuri'u 430,861 yayin da Aisha Dahiru Binani ta APC ta samu kuri'u 398,738.

Ga sakamakon zaɓen nan ƙasa da muka samo

1. Mubi North LGA

APC. 168

PDP. 319

2. Guyuk LGA

APC. 228

PDP. 322

3. Gombi LGA

APC. 12

PDP. 53

4. Mayo Belwa LGA

APC. 478

PDP. 672

5. Toungo LGA

APC: 427

PDP: 360

6. Michika LGA

APC. 562

PDP 1,027

7. Girei LGA

APC. 589

PDP. 444

8. Numan LGA

APC 621

PDP. 1,403

9. Madagali LGA

APC. 47

PDP. 147

10. Mubi South LGA

APC. 253

PDP 298

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng