Jam'iyyar APC Ta Kori Sanata Danjuma Goje Daga Jam'iyyar
- Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a mazaɓar Kashere cikin jihar Gombe ta kori sanata mai ci daga cikin ta
- Jam'iyyar ta kori tsohon gwamnan jihar ta Gombe, Sanata Muhammad Danjuma Goje kan wasu zarge-zarge da ake masa
- Jam'iyyar APC na zargin Sanata Danjuma Goje da yi mata zagon ƙasa a lokacin babban zaɓen 2023
Jihar Gombe - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Gombe ta kori Sanata Muhammad Danjuma Goje, daga jam'iyyar bisa zargin sa da yi mata zagon ƙasa.
Daily Trust ta kawo rahoto cewa, a watan da ya gabata ne jam'iyyar a matakin mazaɓar Sanatan, ta kafa kwamitin bincike akan zarge-zargen cin dunduniyar jam'iyyar da ake yi wa Goje a lokacin babban zaɓen 2023.
Da yake magana da manema labarai a Kashere, shugaban jam'iyyar APC na mazaɓar, Tanimu Abdullahi, yayi bayanin cewa jam'iyyar ta yanke wannan hukuncin ne bagan ta kama Sanatan da laifin yi mata zagon ƙasa.
Ana masa tuhumomi da masu yawa
A kalamansa:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Abubuwan da yayi sun haɗa da ƙin halartar kamfen ɗin jam'iyyar APC na jihar Gombe wanda shugaban jam'iyyar na ƙasa, Abdullahi Adamu, ya jagoranta, ƙin zuwa kamfen ɗin shugaban ƙasa na APC a jihar Gombe, wanda zaɓaɓɓen shugaban ƙasa da mataimakin sa suka halarta."
Abdullahi ya ƙara da cewa ana zargin Sanatan da ƙin zuwa dukkanin tarukan kamfen na jam'iyyar APC a yankin sa, cewar rahoton The Cable
Tanimu ya kuma ƙara da cewa ana zargin sanaatan da yin kalamai waɗanda suka taɓa ƙimar gwamnatin APC a jihar da ɗaukar nauyin yaɗa ƙarya akan gwamnatin jihar da niyyar ɓata mata suna a idon al'ummar jihar.
Shugaban jam'iyyar ya kuma yi zargin cewa Goje ya bayar da umurni ga na kusa da shi da yaran sa cewa shi kaɗai kawai za su zaɓa a inuwar APC, inda ya ce su tabbatar sauran ƴan takarar APC sun yi rashin nasara a zaɓen.
"A dalilin haka shugabannin APC na. mazaɓar Kashere, sun yanke hukuncin korar Sanata Muhammadu Danjuma Goje daga jam'iyyar bisa cin dunduniyar ta da ya yi wanda hakan ya saɓa wa kundin tsarin mulkin jam'iyyar APC." A cewarsa.
Da aka tuntuɓi wani hadimin sanatan wanda ya nemi a sakaya sunan sa, ya ce zancen korar sanatan da jam'iyyar APC a jihar Gombe tayi ya saɓawa hukuncin da wata babbar kotun tarayya tayi.
Sanatan APC Ya Samu Goyon Bayan ‘Yan Majalisar Kano da Jigawa
A wani rahoton na daban kuma, sanatan jam'iyyar APC ya samu goyon bayan ƴan majalisar jihohin Kano da Jigawa a ƙoƙarin sa na samun shugabancin majalisar dattawa.
Sanata Jibrin Barau Maliya, yana daga cikin ƴan majalisar da ke kan gaba wajen neman shugabancin majalisar dattawa ta 10.
Asali: Legit.ng