Kwamishinonin Hukumar Zabe INEC Sun Shiga Taron Gaggawa a Abuja

Kwamishinonin Hukumar Zabe INEC Sun Shiga Taron Gaggawa a Abuja

  • Kwamishinonin INEC na kasa daga jihohin Najeriya baki ɗaya sun shiga ganawar sirri a birnin tarayya Abuja
  • Taron na zuwa ne awanni bayan INEC ta dakatar da kwmaishinan jihar Adamawa, Barista Hudu Yunusa Ari
  • REC din Adamawa ya haddasa cece kuce bayan ya ayyana Sanata Aishatu Ɗahiru Binani a matsayin wacce ta lashe zaɓen gwamna

Abuja - Baki ɗaya kwamishinonin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa sun shiga ganawar sirri yanzu haka a Hedkwatar INEC da ke babban birnin tarayya Abuja.

Hakan na zuwa ne awanni 24 bayan hukumar zaɓe ta umarci kwamishinanta na jihar Adamawa, Hudu Yunusa Ari, ya nesanta kansa daga harkokin hukumar da zaɓen Adamawa.

Farfesa Mahmud Yakubu.
Shugaban INEC ta ƙasa, Farfesa Mahmud Yakubu Hoto: INECNigeria
Asali: UGC

A ranar Lahadin da ta gabata, kwamishinan (REC) ya ta da ƙura da misalin ƙarfe 9:00 na safe lokacin da ya ayyana Sanata Aishatu Binani a matsayin wacce ta lashe zaɓen gwamna.

Kara karanta wannan

Boye-Boye Ya Kare, Ranar Da INEC Za Ta Bayyana Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar Adamawa Ta Bayyana

Channels tv ta rahoto cewa ayyana Binani a matsayin wacce ta ci zaben Adamawa ya haddasa cece-kuce duba da gwamna mai ci, Ahmadu Fintiri, na PDP ne a kan gaba da yawan ƙuri'u.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Amma nan take hukumar zaɓe ta umarci Barista Hudu Ari ya je Abuja kuma ta soke ayyama Binani a matsayin zaɓaɓɓiyar gwamna, wanda za'a iya cewa ya yi wa baturen zaɓe karfa-ƙarfa.

Gabanin INEC ta dakatar da tattara sakamakon, baturen zaɓen Adamawa ya karbi sakamako daga kananan hukumomi 10 cikin 20 da abun ya shafa, kuma Binani ke take wa Fintiri baya a yawan kuri'u.

Ana tsammanin ci gaba da tattara ragowar sakamakon ranar Lahadi da misalin karfe 11:00 na safe, kawai Hudu Ari ya sanar da sakamakon duk da Mele Lamido, baturen zaɓen ba ya wurin.

Kara karanta wannan

Wani Gwamna Ya Dira Yola, Ya Yi Kus-Kus da Fintiri Kan Ayyana Binani a Matsayin Gwamnan Adamawa

A tanadin da ke kunshe a kundin mulkin ƙasar nan, Mele Lamido, ne ke da alhakin bayyana wanda ya lashe zaɓe a jihar Adamawa.

Har iyalaina Obi suka zaɓa - Umahi

A wani labarin kuma Gwamnan APC Ya Tona Asirin Gidansa, Ya Fallasa Yadda Iyalansa Suka Zaɓi Peter Obi a 2023

Gwamna Umahi na jihar Ebonyi ya ce ya yi mamaki sosai bayam gano cewa wasu daga cikin iyalansa Peter Obi suka zaɓa.

A cewar Umahi ya yi mamakin yadda shugaba Muhammadu Buhari da shugaban ƙasa mai jiran gado, Bola Tinubu, suka faɗi a jihohinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262