Jam'iyyar APC Ta Miƙa Sunayen Yan Takarar Gwamna a Jihohi 3 Ga INEC
- APC ta tura sunayen yan takarar da ta baiwa tikitin takarar gwamna a jihohin Imo, Bayelsa da Kogi
- Wannan na zuwa ne bayan jam'iyyar ta kammala zaben fidda gwani a jihohin guda uku
- Ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023 hukumar zaɓe zata gudanar da zaben gwamna a jihohin
Abuja - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta tura sunayen 'yan takararta na gwamna a jihohin Imo, Bayelsa da Kogi zuwa ga hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC).
Wannan na ƙunshe ne a wata takarda da gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta watau TuwitaK da yammacin ranar Lahadi.
Takardan mai ɗauke da adireshin shugaban INEC na ƙasa, Farfesa Mahmud Yakubu, na ƙunshe da sunayen 'yan takarar gwamna a dukkan jihohin uku.
A cewar takardan mai ɗauke da sa hannun muƙaddashin shugaban APC, Sanata Abubakar Kyati da Sakatare, Sanata Iyiola Omisore:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Mun rubuta wannan takarda ne domin aiko da sunayen yan takararmu na gwamna a zaɓen wajen layi dake tafe ga hukumarku"
Jerin 'yan takarar gwamnan APC a jihohin guda uku
A cikin wasiƙar, jam'iyyar APC ta bayyana sunayen mutanen da ta baiwa tikitin takarar gwamna a zaɓen Imo, Bayelsa da Kogi mai zuwa, ga su kamar haka;
1. Mai girma tsohon ƙaramin ministan albarkatun man Fetur, Temipre Sylva - Jihar Bayelsa.
2. Mai girma gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma - Jihar Imo
3. Ahmed Ododo - jihar Kogi.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa a ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023, INEC zata gudanar da zabem gwamna a waɗan nan jihohi guda uku.
Gwamna Uzodinma na kokarin zarcewa kan madafun iko a jihar Imo yayin da Ahmed Ododo, wanda ke da goyon bayan gwamna mai ci, ke neman zangon farko a Kogi.
Sylva, tsohon ƙaramin ministan man Fetur na da jan aiki a gabansa, inda zai gwabza da gwamna mai ciki Douye Diri na PDP a yunkurinsa na kwace mulkin Bayelsa.
A wani labarin kuma Jam'iyyar APC Ta Lashe Kujerun Yan Majalisu 8 a Cikon Zaben Jihar Kebbi
Bayan ta lashe kujerar gwamna tun da fari, APC ta ci gaba da samun nasara a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Asali: Legit.ng