Abubuwan Sani Dangane Da Halin Da Ake Ciki Kan Zaben Gwamnan Adamawa

Abubuwan Sani Dangane Da Halin Da Ake Ciki Kan Zaben Gwamnan Adamawa

Jihar Adamawa - An samu tashin hankula a jihar Adamawa ranar Lahadi, lokacin da kwamishin hukumar zaɓe ta INEC na jihar, Farfesa Hudu Yunusu-Ari ya sanar da Aisha Binani ta jam'iyyar APC a matsayin wacce ta lashe zaɓen gwamnan jihar.

Rahoton Channels tv ya bayyana cewa sanarwar bata yi wa mutanen da suke a wajen bayyana sakamakon daɗi ba, wanda har barazana ta kawo ga zaman lafiyar jihar.

Abubuwan sani kan zaben gwamnan Adamawa
Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri da Aisha Binani Hoto: Channels Television
Asali: Twitter

A yayin da ake ta ci gaba da zaman ɗar-ɗar a jihar, ga jerin wasu abubuwa muhimman abubuwa da mu ka sani zuwa yanzu.

1. Hudu Yunusa-Ari baya da hurumin bayyana sakamakon zaɓen

Abu na farko dangane da lamarin shine, kwamishinann zaɓen baya da hurumin sanar da Aisha Binani a matsayin wacce ta lashe zaɓen. Alhakin hakan yana a akan baturen zaɓen jihar ne, Mr Mele Lamido.

Kara karanta wannan

Adamawa: Hukumar INEC Ta Kasa Ta Yi Karin Haske Kan Ayyana Binani a Matsayin Sabuwar Gwamna

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar INEC, abinda Farfesa Hudu yayi kwace ikon da Lamido yake da shi ne.

2. Baturen zaɓen baya nan aka sanar da sakamakon zaɓen

A lokacin da kwamishinan zaɓen ya bayyana Aisha Binani a matsayin wacce ta yi nasara, baturen zaɓen baya nan a wajen, wanda hakan ya sanya wasu ke tunanin akwai rigima a tsakanin jami'an biyu dangane da sakamakon zaɓen.

3. INEC tace sanarwar bata da amfani

Dangane da matsayar hukumar zaɓe kan lamarin, shugabancin INEC na ƙasa ya bayyana cewa sanarwar da ke nuna cewa Aisha Dahiru Binani, ta lashe zaɓen ta soke ta.

4. An dakatar da tattara sakamakon zaɓen

INEC ta bayyana cewa kwamishinan zaɓen ba wai kawai ya ƙwace ikon baturen zaɓen bane, ya kuma yi gaban kansa ya sanar da wanda ya lashe zaɓen ba tare da an kammala tattara sakamakon zaɓen ba.

Kara karanta wannan

Ruɗani Yayin da INEC Ta Ayyana Aisha Binani A Matsayin Wacce Ta Lashe Zaben Gwamnan Adamawa

A halin da ake ciki INEC ta dakatar da tattara sakamakon zaɓen na cike gurbin da aka gudanar.

5. Ya zuwa daren ranar Asabar, Fintiri ne ke a kan gaba

Kafin a dakatar da tattara sakamakon zaɓen a daren ranar Asabar, an bayyana sakamakon zaɓen daga ƙananan hukumomi 10, wanda a ciki Ahmadu Fintiri na jam'iyyar PDP ke kan gaban Aisha Binani.

6. Ana jiran sauran ƙananan hukumomi 10

Har ya zuwa ƙarfe 11 na safiyar ranar Lahadi, ana jiran a ci gaba da tattara sakamakon zaɓen na ragowar ƙananan hukumomi 10.

7. Jam'iyyar PDP ta nemi da a cafke kwamishinan zaɓen

Jam'iyyar PDP ta yi kiran da a cafke kwamishinan zaɓen sannan a gudanar da bincike domin gano ko su waye yake yi wa aiki, cewar rahoton The nation

Jam'iyyar ta kuma yi kira ga ƴan Najeriya da su yi fatali da sanarwar.

8. Binani ta yi jawabin murnar lashe zaɓe

Kara karanta wannan

Daga karshe: Bayan dogon kai ruwa rana, Ado Doguwa ya lallasa dan tsagin Kwankwaso

A halin da ake ciki, Binani ta gabatar da jawabin murnar lashe zaɓe jim kaɗan bayan an bayyana ta ba bisa ƙa'ida ba, a matsayin zaɓaɓɓiyar gwamnan jihar.

A jawabin na ta, ta godewa mutanen jihar bisa zaɓar ta da suka yi. A cewar ta, zamanta gwamna mace ta farko da aka zaɓa a Najeriya, zai ƙara ƙarfafa guiwar mata su tsunduma cikin harkokin siyasa.

9. Gwamna Fintiri baya fargaba

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya bayyana cewa yana da ƙwarin guiwar cewa zaɓen gwamnan jihar ba za ayi wata ƙumbiya-ƙumbiya ba, duba da kayan fasahar da hukumar INEC ta yi amfani da su.

Ya ce dukkanin sakamakon zaɓen daga rumfunan zaɓe 69 an ɗora shi akan fotal ɗin duba sakamakon zaɓe na INEC, wato IReV.

Shugaba Buhari Ya Sanya Baki a Rikicin Sudan, Ya Aike Da Wani Muhimman Sako

A wani rahoton na daban kuma, kun ji yadda shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya yi wani muhimmin kira kan rikicin da ya ɓarke a ƙasar Sudan.

Shugaba Buhari ya nemi ɓangarorin biyu masu faɗa da juna da su ajiye makaman su, su hau kan teburin sulhu domin kawo ƙarshen rikicin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng