Gwamnonin APC Sun Cire Mutum 2 da 'Yan Arewa a Cikin Masu Harin Shugaban Majalisa
- A kwanakin baya Gwamnonin APC suka yi taro, kuma su ka aikawa Bola Tinubu matsayar 'Yan PGF
- Abin da Gwamnonin suke so shi ne jam’iyya mai mulii ta ware yankin da za su rike mukamai a majalisa
- Idan aka bi shawararsu, shugaban majalisar dattawa ba zai fito daga jihohin Arewacin Najeriya ba
Abuja - Gwamnonin da ke mulki a karkashin jam’iyyar APC sun bada shawarar a ware bangarorin da za a ba shugabanci a majalisar tarayya ta goma.
Kamar yadda Premium Times ta fitar da rahoto, wadannan Gwamnoni sun ba Bola Tinubu shawara a kai shugabancin majalisar dattawa zuwa Kudu ne.
Daga kudu maso kudu ko Kudu maso gabas ake so a samu wanda zai rike majalisar dattawa.
Gwamnonin sun kawo shawara cewa wanda zai zama sabon shugaban majalisar wakilai ya fito daga Arewa maso yamma ko dai Arewa maso tsakiya.
Za ayi sakayya ga wadanda suka bi jam'iyya
Idan aka yi haka, sai a raba mukaman shugaban masu rinjaye da mataimakinsa da mai tsawatarwa da mataimakinsa ga wadanda suka janye takararsu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Takardar da Gwamnonin nan suka aikawa zababben shugaban kasar a ranar 8 ga watan Afrilu ta shiga hannun jaridar, an ji labarin abin da ta kunsa.
Yadda rabon kujerun zai kasance
a. Shugaban majalisar dattawa - Kudu maso kudu ko Kudu maso gabas
b. Mataimakin Shugaban majalisar dattawa - Arewa maso yamma ko Arewa maso tsakiya
c. Shugaban majalisar wakilai - Arewa maso yamma ko Arewa maso tsakiya
d. Mataimakin Shugaban majalisar wakilai - Kudu maso kudu ko Kudu maso gabas
Atiku Bagudu ya sa hannu a wannan takarda a madadin sauran ‘yan kungiyar Gwamnonin APC, sai dai har yanzu Tinubu yana hutawa a kasar waje.
Rahoton ya kara da cewa an yi fatali da mutane biyu daga cikin masu harin zama shugaban majalisa, dalili kuwa shi ne ‘yan majalisa na da dokokinsu.
Babu Sanatocin da za su wakilci Ebonyi da Edo, Dave Umahi da Adams Oshiomhole ba za su shiga takarar ba saboda yanzu ne karonsu na farko a majalisa.
Ana maganar irinsu Orji Uzor Kalu, Osita Izunaso da Godwill Akpabio a tseren na bana ne, kowanensu ya yi akalla shekaru hudu kenan yana majalisa.
Kafin nan, an ji labari wasikar da Gwamnonin APC suka rubutawa Bola Tinubu ta nuna dole a dauki mataki a Majalisa kafin a ga abin da ya faru a 2015.
Ana zargin cewa masu takara a Majalisar Najeriyan sun shirya batar da $500, 000-$1m a matsayin cin hanci a kan kowace kuri’a da za su iya samu.
Asali: Legit.ng