“Ka Fada Mana Gaskiya”: Wasu Kattan Maza Sun Tube Kwamishinan Zabe Na Kasa a Adamawa

“Ka Fada Mana Gaskiya”: Wasu Kattan Maza Sun Tube Kwamishinan Zabe Na Kasa a Adamawa

  • Wasu mutane da ba a san ko wanene ba a jihar Adamawa sun tube wani kwamishinan zabe na kasa a cikin wani bidiyo da ya yau inda aka yi wa dattijon tambayoyi
  • Cikin harshen Hausa, an jiyo kattan mazan da ba a san ko wanene ba suna umurtan kwamishinan da ya fadi gaskiya
  • Tun farko INEC ta nuna damuwarta game da cin zarafin kwamishinoninta na kasa da aka tura don tabbatar da zaben ciko na lumana da gaskiya a Adamawa

Adamawa - Wasu mutane da ba a san ko wanene ba a jihar Adamawa sun tube wani kwamishinan hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wanda aka sakaya sunansa.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an gano wasu mutane suna yi wa dattijon tambayoyi a cikin wani bidiyo da ya yadu.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Malamin Kwaleji Ya Dauki Jinjirin Dalibarsa Cike Da Sakin Fuska Ya Yadu, Jama’a Sun Jinjina Masa

Shugaban hukumar zabe ta kasa, Farfesa Yakubu Mahmood
“Ka Fada Mana Gaskiya”: Wasu Kattan Maza Sun Tube Kwamishinan Zabe Na Kasa a Adamawa Hoto: Olukayode Jaiyeola/NurPhoto
Asali: Getty Images
"Ka fada mana gaskiya sannan za mu kyaleka da ranka," daya daga cikin kantan manzan ya furta cikin bayar da umurni."

An kuma jiyo wani yana umurtan dattijon da "sa wandonka", wanda jami'in zaben ya ya girgiza kansa sannan ya furta wasu kalamai da basu fita da kyau ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Za mu taimaka maka idan ka fada mana gaskiya," cewar wani mai masa tambayoyi.

Legit.ng ta tattaro cewa sun yi duk wannan maganganun ne a cikin harshen hausa da turanci kadan-kadan.

An jiyo wata murya a kasar bidiyon tana cewa:

"Wannan ba shine baruren zaben INEC ba. Shi jami'i ne na kasa."

Yadda ake cin zarafin kwamishinonin INEC na kasa

Ku tuna cewa hukumar INEC ta koka a baya cewa ana cin zarafin kwamishinoninta na kasa.

A wata sanarwa da kakakin hukumar, Festus Okoye ya fitar, ya yi kira ga hukumomin tsaro da su samar da tsaro ga jami'an zabe.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Gobara Ta Tashi Ana Tsaka Da Shagalin Bikin Aure, Jama'a Sun Ci Na Kare

INEC ta nesanta kanta daga ayyana Aisha Binani a matsayin zababbiyar gwamnar Adamawa

A baya mun ji cewa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta soke ayyana Aisha Dahiru Binani a matsayin zababbiyar gwamna a jihar Adamawa.

Hukumar zaben ta kasa ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Twitter a ranar Lahadi, 16 ga watan Afrilu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng