Karin Bayani: Baturen Zaben INEC Ya Ayyana Aisha Binani A Matsayin Wacce Ta Lashe Zaben Gwamnan Adamawa
- Kwamishinan hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) na jihar Adamawa ya sanar da sakamakon zaɓen gwamna
- Lamarin dai ya haddasa cece kuce a faɗin Najeriya saboda har yanzu ba'a kammala tattara sakamakon cikon zaɓen ba
- Tuni dai INEC ta soke sakamakon da kwamishinanta ya bayyana kana ta kira shi zuwa Abuja kuma ta dakatar da tattara sakamakon
Jihar Adamawa - Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta ayyana Sanata Aisha Dahiru, da aka fi sani da Binani, a matsayin wacce ta lashe zaben gwamna na jihar Adamawa, Daily Trust ta rahoto.
An sanar da sakamako daga kananan hukumomi 10 cikin 20 a yayin da aka dakatar da cigaba da sanar da sakamakon zuwa karfe 11 na safe.
Amma, Ari ya sanar da sakamakon karshe na zaben awa guda kafin ainihin lokacin da aka shirya.
Legit.ng ta tattaro cewa Gwamna Ahmadu Fintiri na jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP shine ke kan gaba kafin sanarwar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
An ji wasu magoya bayan jam'iyyar PDP a dakin taron da baturen zaben ya sanar da sakamakon zaben suna nuna cewa ba su yarda ba.
Jaridar Nigerian Tribune ita ma ta rahoto sanarwar sakamakon zaben da ya janyo cece-kuce daga kowane ɓangare na kasar nan.
INEC ta soke ayyana Binani a matsayin wacce ta samu nasara
Amma a wata sanarwa da Festus Okoye, kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kan masu kaɗa kuri'a ya rattaɓa wa hannu, INEC ta nesanta kanta da abinda REC ɗin Adamawa ya aikata.
INEC ta soke sakamakon da REC ɗin ya bayyana kuma ta umarce shi da ya kai kansa birnin tarayya Abuja.
Wannan na zuwa ne bayan zaben cike gurbin da aka gudanar ranar Asabar 15 ga watan Afrilu, 2023 a sassan ƙasar nan.
INEC ta bayyana wanda ya ci zaben gwamna a jihar Kebbi
A wani labarin kuma INEC ta bayyana ɗan takarar gwamna a inuwar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen jihar Kebbi
Dakta Nasiru Idris na jam'iyyar APC ya samu nasarar lallasa babban abokin karawarsa na jam'iyyar PDP, Aminu Bande, bayan kammala tattara sakamako ranar Lahadi.
Asali: Legit.ng