Jerin Waɗanda Suka Lashe Cikon Zabe a Kaduna, Katsina da Wasu Jihohin Arewa 2
A yau Asabar 15 ga watan Afrilu, 2023, INEC ta gudanar da zaben cike gurbi a wasu mazabun yan majalisun jihohi da na tarayya a faɗin ƙasar nan.
A jihar Kaduna, cikon zaɓen ya gudana a mazaɓun mambobin majalisar dokokin jiha guda huɗu, wanda ya kunshi, Kauru, Giwa, Kudan da kuma Sanga.
Haka a jihar Katsina, mazaɓun yan majalisar jiha uku zaɓen yau ya shafa, sun haɗa da, mamba mai wakiltar Kankiya, mamba mai wakiltar Kanƙara da kuma ɗan Majalisar Kurfi.
A wannan shafin, Legit.ng Hausa zata kawo muku sakamakon cikon zaben waɗan nan mazaɓu na Kaduna da Katsina, da kuma na jihar Zamfara, Daily Trust ta rahoto.
APC ta lashe zaɓen Gumel a jihar Jigawa
Hukumar zaɓe INEC ta ayyana Sani Nazifi na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya ya lashe zaɓen ɗan majalisar tarayya a zaben cikon da aka kammala ranar Asabar.
Nazifi, wanda ke wakiltar mazaɓar Gumel-Gagarawa-Suletankar-Maigatari a majalisar wakilan tarayya ta lashe kujerar a karo na biyu.
Baturen zaɓen INEC, Farfesa Ahmed Baita, lokacin sanar da sakamakon a Gumel, ya ce Nazifi ya samu kuri'u 49,893, inda ya lallasa babban abokin adawarsa Ahmed Habu na PDP, wanda ya samu kuri'a 46,537.
PDP ta ƙara samun nasara a jihar Zamfara
Jam'iyyar PDP ta ci gaba da jan zarenta a jihar Zamfara, ta lashe kujerar ɗan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar Gummi / Bukkuyum.
Hukumar zaɓe ta sanar da cewa ɗan takara a inuwar PDP, Sulaiman Gummi, ya samu kuri'u 35, 664, ya samu nasara kan babban abokin gwabzawarsa na kusa, Ahmad Muhammad, na APC mai kuri'u 35,058.
Ɗan takarar PDP ya lashe zaɓen mamban majalisar wakilan tarayya a Zamfara
Bayan kammala zaɓe ranar Asabar 15 ga watan Afrilu, 2023, ɗan takarar jam'iyyar PDP ya lashe zaɓen ɗan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar mazaɓar Gusau/ Tsafe a jihar Zamfara.
INEC ta sanar da cewa Ahmadu Kabiru Mai Palace na PDP ya samu kuri'u 63, 598, inda ya tumurmusa babban abokin karawarsa na APC, tsohon kakakin majalisar dokokin Zamfara, Alhaji Sanusi Garba Rikiji, mai kuri'a 52,495.
PDP ta ci kujerar Sanata a Zamfara
Ɗan takarar jam'iyyar PDP, Aliyu Ikira Bilbis, ya lallasa takwaransa na jam'iyar APC, Kabiru Marafa, a zaɓen Sanatan Zamfara ta tsakiya wanda aka ƙarisa ranar Asabar.
Bilbis na PDP ya samu kuri'a 102, 866 wanda suka ba shi damar kayar da Sanata Marafa na jam'iyyar APC, wanda ya tashi da kuri'u 91,216.
APC ta lashe zaben mazaɓar Kudan a jihar Kaduna
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ayyana Abbas Faisal na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen ɗan majalisar dokokin jiha mai wakiltar Kudan a Kaduna.
Baturen zaben mazaɓar, Farfesa Dauda Aminu, shi ne ya sanar da sakamakon zaɓen a Hunƙuyi ranar Lahadi, ya ce Faisal ya samu kuri'u 22,993, inda ya lallasa Nura Abdulkarim na PDP, wanda ya ci kuri'u 22,878
Jam'iyyar APC ta lashe zaɓen Dutse a Jigawa
Ɗan takarar kujerar majalisar dokokin jiha mai wakiltar Dutse a jihar Jigawa karkashin inuwar APC, Ishaq Tasiu, ya lashe zaɓen cikon da aka kammala ranar Asabar.
Baturen zaɓe a mazaɓar Dutse, Farfesa Ahmad Shehu Kutama, ya ce ɗan takarar APC ta samu nasara a zaben da kuri'u 31,311 yayin da mai biye masa, Alhaji Musa Zai, na PDP ta tashi da ƙuri'a 28,656.
PDP ta lashe kujerar ɗan majalisa a Jigawa
INEC ta ayyana ɗan takarar PDP a mazaɓar Birnin Kudu, Ibrahim Kabiru, a matsayin wanda ya ci zaɓen ɗan majalisar dokokin jihar Jigawa.
Farfesa Usman Haura na jami'ar tarayya da ke Dutse, ya bayyana Kabiru a matsayin wanda ya lashe zaɓen Birnin Kudu da kuri'u 36,050.
Ya samu nasarar lallasa babban abokin adawarsa kuma ɗan majalisa mai ci na jam'iyyar APC, Muhammad Surajo, wanda ya samu kuri'u 34,545.
APC ta lashe zaben Sanga a Kaduna
Hukumar zaɓe INEC ta bayyana Haliru Dangana na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen ciko na mamban majalisar dokokin jiha mai wakiltar Sanga a jihar Kaduna.
Baturen zabe, Farfesa Ibrahim Musa ga sanar cewa Dangana ya samu kuri'u 13,883, inda ya lallasa babban abokin gwabzawarsa na PDP, Comfort Amwe, wanda ya tashi da kuri'u 13,275.
APC ta lashe 2 PDP ta ci 1 a zaben mambobin majalisar dokokin Katsina 3
Jam'iyyar APC ta lashe zaben ɗan majalisar dokokin jiha mai wakiltar Kankia bayan kammala tattara sakamakon zaben da aka karisa ranar Asabar.
INEC ta ayyana Salisu Rimaye na APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen da kuri'u 18, 157, ya lallasa Abdullahi Ibrahim na PDP mai kuri'u 16, 763.
Bugu da ƙari, APC ta lashe kujerar Kurfi yayin da babbar jam'iyyar hamayya PDP ta ci kujerar Kankara duk a majalisar dokokin jiha.
APC ta lashe zaben Giwa a Jihar Kaduna
Honorabul Awwal Umar na jam'iyyar APC ya lashe zaɓen cikon da aka kammala a mazaɓar ɗan majalisar dokokin jiha mai wakiltar Giwa ta yamma a jihar Kaduna.
Da take bayyana sakamakon zaɓen, Farfesa Maryam Suleiman, jami'ar INEC ta sanar da cewa:
"Bayan cika sharuddan doka kuma ya samu kuri'u mafiya rinjaye, Awwal Umar na jam'iyyar APC ya lashe zaɓen kuma ya zama zababbe."
Farfesa Maryam ta bayyana cewa ɗan takarar APC ya samu kuri'u 15,603 ya lallasa babban abokin karawarsa na jam'iyyar PDP, Bello Muazu, wanda ya tashi da kuri'u 14,897.
Sakamakon cikon zaben Sanata da yan majalisar wakilai a Zamfara
Mazabar Mayana 073, Kofar gidan Malam Murtala Zawiyya.
Sakamakon zaben Sanata
PDP. 51
APC. 37
Mamban majalisar wakilai
PDP. 55
APC. 32
MADA WARD 023
Sakamakon Zaɓen mamban majalisar wakilai ta ƙasa
APC 47
PDP 70
Sakamakom Zaben Sanata
APC 50
PDP Sen 65
MADA (Ɗan Hili)
Sakamakon zaɓen Sanata
APC- 38
PDP- 77
Sakamakon zaben ɗan majalisar wakilan tarayya
APC- 40
PDP- 73
Sabon Gari 005 (Stadium)
Sakamakon zaben Sanata
APC: 89
PDP: 94
Sakamakon zaben ɗan majalisar wakilai
APC: 89
PDP: 92
Gidan Tudu/ Tudun Wada 068
Sakamakon zaben Sanata
PDP 30
APC 24
Sakamakon zaben ɗan majalisar wakilai
APC 35
PDP 32