Yan Daba Sun Sace Akwatun Zabe Yayin Zaben Cike Gurbi a jihar Imo
- Mazauma karamar hukumar Isu ta jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya sun shiga tashin hankali
- An tattaro cewa ana tsaka da cikon zaɓe a karamar hukumar, wasu yan daba suka kutsa kai rumfar zaɓe suka sace Akwatu
- Wani ganau ya ce 'yan daban sun farmaki rumfar zaɓen ba tare da wahala ba duk da tulin jami'an tsaron da aka girke a wurin
Imo - Wani shaidan gani da ido ya tabbatar da kai harin kwace Akwatun zaɓe a cikon zaɓen da ke gudana yau a jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya.
Rahoton Vanguard ya bayyana cewa wasu yan daba sun kutsa kai tare da sace Akwatun zaɓe a Umuarusi Amandugba hall, ƙaramar hukuma Isu a jihar Imo.
Bayanai sun nuna cewa ana zargin 'Yan daban sun samu taimakon jami'an tsaron da aka tura wurin, suka kutsa kai cikin sauki kuma suka yi awon gaba da Akwatun zaɓe.
Rahotanni sun bayyana cewa yan daban sun shiga rumfar zaben da misalin ƙarfe 9:19 na safe duk da tulin dakarun tsaron da aka tura tsare kayan zaɓe a mazaɓar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Masu kaɗa kuri'u sun maida martani kan harin
Sai dai tun da fari, masu kaɗa kuri'a a mazaɓar sun nuna damuwa da fargaba bisa ganin tulin jami'an tsaron da suka mamaye rumfar da kuma motocin sulƙe da ke rangadi a wurin.
Wani mai kaɗa kuri'a mai suna Chibuike ya ce:
"Muna jin tsoro, kuna ganin yadda suka sace akwatun zaɓe tare da jami'an tsaron da ke wurin, muna ganin wannan shiryayyen abu ne kawai."
"Mun tsorata kuma hankalin mu ba kwance yake ba. Ta ya za'a gudanar da zaɓe da motocin sulƙe? Wannan ba daidai bane."
Ododo Ya Doke Adeyemi Da Sauransu Wajen Samun Tikitin APC
A wani labarin kuma Daga karshe, An Sanar Da Wanda Ya Lashe Tikitin APC Na Zaben Gwamna a Jihar Kogi
Kwamitin shirya zaɓen fidda gwanin jam'iyyar APC a jihar Kogi ya sanar da wanda ya lashe tikitin takarar gwamna a zabe mai zuwa cikin shekarar nan.
Ahmed Usman Ododo, tsohom Audita janar na jihar ne ya samu nasara da gagarumin rinjaye.
Asali: Legit.ng