Dan Takarar Majalisa Na Jam'iyyar Labour Ya Dauki Hayar Makasa Sun Kashe Abokin Hamayarsa Na PDP A Ebonyi

Dan Takarar Majalisa Na Jam'iyyar Labour Ya Dauki Hayar Makasa Sun Kashe Abokin Hamayarsa Na PDP A Ebonyi

  • Rundunar yan sanda a Ebonyi sun kama dan takarar majalisar jiha a jam'iyyar LP bisa zargin hada kai tare da kisan kai
  • Rundunar ta kama karin mutane uku tare da shi, yayin da ta bayyana cewa tana cigaba da neman karin mutane 21 da ake zargi
  • Rundunar ta ce zata mika wanda ake zargi kotu da zarar ta kammala bincike don girbar abin da su ka shuka

Jihar Ebonyi - Rundunar yan sandan Ebonyi sun kama mutum hudu bisa zargin kashe Peter Nweke, wani shugaban PDP a matakin mazaba, a karamar hukumar Ezza ta arewa da ke jihar.

Ana zargin an yi wa jigon PDPn duka har ta kai ya mutu ranar 18 ga watan Maris yayin da zaben gwamna da na yan majalisa ke gudana a Ebonyi, The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Mayakan Boko Haram Sun Kai Kazamin Hari a Jihar Yobe, Sun Murkushe Mutum 9

Alkali Baba.
Rundunar yan sanda ta Ebonyi ta ce za a gurfanar da dukkan mutane hudun da zarar an kammala bincike. Hoto: NPF HQ
Asali: UGC

Rundunar yan sanda ta fitar da sanarwa kan afkuwar lamarin

Da ta ke zantawa da manema labarai ranar Juma'a a Abakaliki, babban birnin Ebonyi, Onome Onovwakpoyeya, mai magana da yawun yan sandan jihar, ta ce daya daga cikin wanda ake zargi dan takarar majalisar jiha ne a jam'iyyar LP.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta ce wanda ake zargin - Kelechi Nwali, Onyebuchi Chita, Aloke Obinna, da Ifeanyi Nwokpuku an kama su ne ranar 28 ga watan Maris.

The Punch ta rahoto cewa mai magana da yawun yan sandan ta ce ana kuma cigaba da neman mutane 21 da ke da alaka da laifin.

"Biyo bayan wannan mummunan laifi, Kwamishinan yan sanda, CP Falaye S. Olaleye, ya bada umarni ga duk jami'an yan sanda da ke yankin da abin ya shafa da su tabbatar sun kamo masu hannu a kisan," in ji mai magana da yawun yan sanda.

Kara karanta wannan

Kitimurmura: Kotu ta soke wasu tarukan zaben APC da aka yi a jihar Arewa don zabo dan takarar gwamna

"Bisa umarnin, an kama mutane hudu da ake zargi da hannu kan mutuwar Mista Peter Nweke, ranar 28 ga watan Maris.
"Da ake tuhumar wanda ake, na farko, Kelechi Nwali, namiji, dan takarar majalisar jiha a jam'iyyar LP, mazabar Ezza ta arewa, ya amsa daukar hayar tsageru da nufin su azabtar da mamacin, amma, a garin haka sai ya mutu.

Ta cigaba da cewa:

"A cewar Nwali, marigayi Peter Nweke na zame masa barazana ga siyasarsa, sai ya tuntubi wani Akwasi, namiji, na Umuezeoka da ke Ezza ta arewa, wanda ya jagoranci azabtar da shi har ta kai ga mutuwar Nweke.
"Na biyu da ake zargi, Onyebuchi Chita na unguwar Nkomoro, ya amsa dauko shi daga Nkomoro zuwa Ogboji inda aka kashe Nweke.
"Wanda ake zargi na uku, Aloke Obinna na unguwar Ogboji, ya amsa cewa ya bada babur dinsa ga Onyebuchi Chita don ya gudu bayan aikata laifin.
"Yayin da Ifeanyi Nwokpuku, wanda ake zargi na hudu daga unguwar Ogboji, duk a Ezza ta arewa, ya hada da kai da wani Sampson Nweke, namiji, inda suka nuna Peter Nweke ga makasan."

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Sojoji Sun Murkushe Kasurgumin Dan Bindigar Kaduna, Isiya Danwasa

Onovwakpoyeya ta kara da cewa za a tura wanda ake zargi kotu bayan kammala bincike.

An cafke wasu mutane 3 kan lsace wata yarinya a Kano

A wani rahoton yan sandan jihar Katsina sun kama wasu matasa guda uku kan zargin sace wata yarinya yar shekara shida.

Gambo Isah, Kakakin yan sandan Kano cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, ya ce matasan sun hada baki ne wurin sace yarinyar a unguwar Bachirawa da ke Kano a watan Janairu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164