Gwamna Uzodinma Ya Lashe Zaben Fidda Gwanin APC a Jihar Imo
- Kwamitin shirya zaɓen fidda gwani a jihar Imo ya bayyana sakamakon zaɓen da ya gudana ranar Jumu'a
- Ɗan takara ɗaya tilo da ya shiga zaben kuma gwamna mai ci, Hope Uzodinma ne ya samu nasara
- A ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023, za'a gudanar da zaben gwamna a jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya
Imo - Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya lashe zaɓen fidda gwani na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) wanda ya gudana a jihar.
The Cable ta rahoto cewa Uzodinma ne kaɗai ɗan takara a zaɓen fidda gwanin wanda ya gudana ranar Jumu'a a Owerri, babban birnin jihar Imo.
Shugaban kwamitin shirya zaɓen, Williams Kayoda, ya sanar da sakamko cewa gwamna Uzodinma ya samu kuri'u 63,618 wanda suka ba shi damar lashe zaɓen.
Ya ce adadin Deleget 64,667 daga gundumomi 305 a kananan hukumomi 27 na jihar Imo aka tantance domin kaɗa kuri'a a lokacin zaɓen.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"A ɗan kankanin lokacin da muka zauna a Imo, mun naɗa kwamitocin kananan hukumomi sabida zaɓen. Nauyin da aka ɗora mun na tabbata an bi tsarin demokaraɗiyya."
"Ya rataya a wuyana na tabbatar zaɓen ya gudana bisa tsarin kundin mulkin kasa, bai sauka daga kan doka ba, kuma mutane su yi na'am da zaɓen."
"Dogaro da wannan, mun gudanar da zaɓen fidda gwani ta tsarin kato bayan ƙato a dukkan kananan hukumomi 27."
- Williams Kayoda.
Bayan haka Kayoda ya bayyana zaɓen a matsayin wanda ya gudana cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali kuma mai sahihanci.
Wannan nasara ce daga Allah - Uzodinma
A jawabin godiya, gwamna Uzodinma ya gode wa Deleget ɗin jam'iyyarsa ta APC bisa kwarin guiwar da suka nuna a kansa.
Premium Times ta rahoto gwamnan na cewa:
"Na sadaukar da nasarar da muka samu a taron yau ga Allah mai girma kuma nasara ce da zan riƙa tunawa a rayuwata."
"A wurina, ina kallon wannan nasara a matsayin wata alama da ke nuna har yanzu mambobin jam'iyyar mu da ɗaukacin mazauna Imo sun aminta da mu."
APC ta dauki mataki kan mai cin amanarta a Kebbi
A wani labarin kuma Jam'iyyar APC Ta Dakatar da Ɗan Majalisar Wakilan Tarayya a Jihar Kebbi
Jam'iyyar APC mai mulki ta dakatar dan majalisar wakilan tarayya bayan samun korafe-korafe kansa da zargin yana mata zagon ƙasa a jihar Kebbi.
Lamarin na zuwa ne yayin da jam'iyyar ke tunkarar karishen zaɓen gwamna a jihar, ta ce zata gudanar da bincike.
Asali: Legit.ng