Kai Tsaye: An Fara Cikon Zaben Gwamnoni a Jihohi Adamawa Da Kebbi

All posts
Key Events
Analysis
Exclusive
12 Posts
Sort by
Our live updates have concluded for the day. Catch up on everything you missed below.
Aisha Musa avatar Ahmad Yusuf avatar
daga Aisha Musa and Ahmad Yusuf

Sojoji sun harbe ɓarawan Akwati har lahira a Kebbi

Sojojin Najeriya sun bindige wani barawom akwatu a rumfar zaɓe Bajida 001, ƙaramar hukumar Fakai a jihar Kebbi.

Vanguard ta rahoto cewa Sojojin sun harbe mutumin har lahira yayin da ya yi yunkurin kwace Akwatun zaɓe daga wurin Malaman zaben INEC sa'ilin zaben cike gurbin da ke gudana a wasu sassan jihar.

A cewar ganau, mamacin mamba ne a ƙungiyar jami'an tsaron 'Yan Sakai, watau dakarun 'yan banga a yankin

Aisha Musa avatar Ahmad Yusuf avatar
daga Aisha Musa and Ahmad Yusuf

Unguwan Barmani 1, gundumar Kashini, Agwara LGA

Jama'a sun fara kaɗa kuri'a tun da misalin karfe 8:30 na safe a wannan rumfa kuma komai na tafiya a tsanake ba tare da samun cikas ba, jami'an tsaro na sa ido.

Aisha Musa avatar Ahmad Yusuf avatar
daga Aisha Musa and Ahmad Yusuf

Zabe na gudana a Adamawa yayin da aka ji shiru daga jihar Kebbi

PU018, Sangere, Namtari, karamar hukumar Yola ta kudu.

Ana ci gaba da tantance masu zabe da kada kuri’u a wannan rumfar zaben amma sam tsarin baya tafiya yadda ya kamata bisa tsari.

A halin da ake ciki, babu wani sahihin rahoto da ke fitowa daga jihar Kebbi inda ake sa ran cikon zaben gwamna zai gudana a jihar ma a yau.

Aisha Musa avatar Ahmad Yusuf avatar
daga Aisha Musa and Ahmad Yusuf

PU009, Malkohi Primary School, Namtari, Yola South LGA, Adamawa

Zaɓe ya kankama a wannan rumfa ta 009, karamar hukumar Yola ta kudu a jihar Adamawa amma babu tsari mai kyau.

Zaben Adamawa.
Kai Tsaye: An Fara Cikon Zaben Gwamnoni a Jihohi Adamawa Da Kebbi
Source: UGC

Aisha Musa avatar Ahmad Yusuf avatar
daga Aisha Musa and Ahmad Yusuf

Ko Gawa Zamu Ɗauko Daga Makabarta Ta Zaɓi Binani - Mazaunin Adamawa

Wani mai goyon bayan ƴar takarar gwamna karkashin inuwar APC, Aishatu Binani, ya ce Sanata Binani ce zata lashe zaɓe a mazaɓarsa.

A wani budiyo da The Cable ta wallaha, mutumin ya yi ikirarin cewa ko gawa zasu ce su ɗauko a makabarta ta zo ta zaɓi Binani don ta ci zaɓen rumfarsa in sha Allahu.

Aisha Musa avatar Ahmad Yusuf avatar
daga Aisha Musa and Ahmad Yusuf

Ba a fara zabe ba a rumfuna 14 a karamar hukumar Numan, jihar Adamawa

Ba a fara zabe ba a rumfunar zabe 14 a karamar hukumar Numan ta jihar Adamawa, kamar yadda Channels TV ta rahoto.

Da karfe 11:47am, a gudunmar Bolki inda ake da rumfunan zabe 13, an gano jami’an INEC suna tantance kayan zabe don rabawa rumfunan.

Legit.ng ta tattaro cewa a yayin zaben ranar 18 ga watan Maris, ba a yi zabe ba a Bolki saboda matsalar rashin zuwa jami’an INEC da kayan zabe da wuri.

Aisha Musa avatar Ahmad Yusuf avatar
daga Aisha Musa and Ahmad Yusuf

PU 018, Sangere, Namtari, Yola south LGA, Adamawa

Tantance masu kaɗa kuri'a da dangwala zaɓe ya kankama a rumfar PU O18, karamar hukumar Yola ta kudu a jihar Adamawa. Sai dai zaɓen na tafiya babu tsari.

Zabe ya kankama a Adamawa.
Zaben na cigaba da tafiya a Adamawa Hoto: thecable
Source: UGC

Aisha Musa avatar Ahmad Yusuf avatar
daga Aisha Musa and Ahmad Yusuf

Rikici ya kaure wajen zabe a Adamawa

An caki wata matashiya a rumfar zabe na PU006, Kofar Jauro Audu, Jambutu, karamar hukumar Yola ta arewa a Adamawa. Wadanda suka farmaketa sun kwace wayarta. Ba a san dalilin kai mata harin ba.

Hakazalika, an caki wani mutum da ba a san ko wanene ba wata rumfar zabe a karamar hukumar Yola ta arewa saboda yana dauke da kudi a aljihunsa.

Aisha Musa avatar Ahmad Yusuf avatar
daga Aisha Musa and Ahmad Yusuf

Kayan zabe basu isa wasu rumfuna ba a Adamawa

Rahoto ya nuna har zuwa ƙarfe 10:13 malaman zaɓe da kayayyakin zaɓe ba su karisa rumfa ta 0015, gundumar Michika II, karamar hukumar Michika ba.

Aisha Musa avatar Ahmad Yusuf avatar
daga Aisha Musa and Ahmad Yusuf

An sha yar dirama a rumfar zabe na PU004, Bubakari Maigari, Ajiya, karamar hukumar Yola ta Arewa

Jaridar The Cable ta rahoto cewa wakilin wata jam’iyya, ya haddasa cece-kuce yayin da ya yi kokarin taimakawa wata dattijuwar mata kada kuri’arta.

A halin da ake ciki, zabe na gudana a PU006, Kofar Jauro Audu, Jambutu, karamar hukumar Yola ta arewa.

Aisha Musa avatar Ahmad Yusuf avatar
daga Aisha Musa and Ahmad Yusuf

An fara kada kuri’u a jihar Adamawa

An fara tantance masu zabe da kada kuri’u a jihar Adamawa, musamman a rumfunan zabe kamar haka:

PU001, Buba Jalo, Ajiya, karamar hukumar Yola ta arewa, Adamawa

PU004, Bubakari Maigari, Ajiya, karamatr hukumar Yola ta arewa, Adamawa

Aisha Musa avatar Ahmad Yusuf avatar
daga Aisha Musa and Ahmad Yusuf

Manyan yan takara da kallo ke kansu a cikon zaben gwamnoni

Ahmadu Fintiri

Gwamnan jihar Adamawa kuma dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Aisha Dahiru

Sanata kuma yar takarar gwamna na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Adamawa.

Nasiru Idris

Dan takarar gwamnan APC a jihar Kebbi wanda ke kan gaba kafin a ayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba.

Janar Aminu Bande

Dan takarar gwamnan PDP a jihar Kebbi. Ana sa ran zaben cikon zai zamo tsakanin Bande da Idris.

Karanta karin bayani game da manyan yan takarar a nan.