Hukumar INEC Ta Fara Raba Kayayyakin Aikin Zabe a Adamawa

Hukumar INEC Ta Fara Raba Kayayyakin Aikin Zabe a Adamawa

  • Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta shirya tsaf domin gudanar da zaɓen cike gurbi na gwamnan Adamawa
  • Hukumar zaɓen ta fara rarraba kayayyakin aikin zaɓen cike gurbin gwamnan jihar na ranar Asabar
  • Hukumar ta kuma yi wani muhimmin kira ga magoya bayan jam'iyyu da su bi doka da oda lokacin zaɓen

Jihar Adamawa - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) a jihar Adamawa ta fara rabon kayayyakin zaɓe a wuraren da za a gudanar da zaɓen cike gurbi na gwamnan jihar a ranar Asabar.

Hukumar INEC ta bayyana zaɓen gwamnan jihar na watan Maris a matsayin wanda bai kammalu ba, domin yawan katin zaɓen da aka karɓa a wuraren da aka soke zaɓen ya zarce tazarar da aka bayar a zaɓen.

INEC ta kammala rabon kayan aikin zaɓen gwamnan Adamawa
Shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC), Farfesa Mahmud Yakubu Hoto: Premium times
Asali: UGC

Fafatawar dai ta fi zafi ne a tsakanin Sanata Aishatu Binani ta jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da gwamnan jihar mai ci yanzu, Ahmadu Umar Fintiri na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), wanda ya ke kan gaba da ƙuri'u 30,000.

Kara karanta wannan

Abu Ya Girma: Jam'iyyar APC Ta Dakatar da Ɗan Majalisar Tarayya Kan Babban Abu 1

Jaridar Daily Trust ta ce kwamishinonin zaɓen biyu hukumar INEC na ƙasa, Farfesa Abdullahi Abdulzuru da Dr. Baba Bola, suna wajen domin sanya ido kan yadda rabon kayayyakin zaɓen yake gudana a ranar Juma'a.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da yake tattaunawa da ƴan jarida, kwamishinan zaɓen INEC na jihar, Barr. Hudu Ari, ya ce hukumar ta shirya tsaf sannan tana fatan zaɓen ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana.

“Dukkanin kayayyakin aikin zaɓen an raba su. Za su isa zuwa wuraren da ake buƙatar su cikin lokaci." A cewar sa

Ari ya kuma bayyana cewa ƙananan hukumomin da za a yi zaɓen ƴan majalosae dpkokin jihar sune, Girei, Gombi, Numan da Toungo, a cewar Vanguard

Kwamishinan ya kuma roƙi magoya bayan jam'iyyu da su ƙauracewa tayar da kowane irin hargitsi sannan su kasance masu bin doka da oda a lokacin zaɓen da bayan an kammala zaɓen.

Kara karanta wannan

Ana Dab Da Zabe, PDP Ta Bankado Shirin Yi Wa Dan Takarar Gwamnanta Magudi a Adamawa

PDP Ta Bankado Shirin Yi Wa Dan Takarar Gwamnanta Magudi a Adamawa

A wani rahoton na daban kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP tana zargin ana ƙoƙarin yi wa ɗan takarar gwamnanta na jihar Adamawa magudi a zaɓen cike gurbin gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng