Gwamna Tambuwal Ya Nada Sabbin Ciyamomi a Kananan Hukumomi 23

Gwamna Tambuwal Ya Nada Sabbin Ciyamomi a Kananan Hukumomi 23

  • Gwamna Aminu Tambuwal na Sakkwato ya naɗa sabbin shugabannin kanann hukumomi na rikon kwarya
  • Wannan na zuwa ne bayan jam'iyyar PDP ta gwamna mai ci ta sha kaye hannun APC a zaɓen da ya gabata
  • Sakataren gwamnatin jihar ya bayyana sunayen sabbin Ciyamomin da lokacin da zasu fara aiki

Sokoto - Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya naɗa Ciyamomin riko a kananan hukumomi 23 da ke faɗin jihar ta arewa maso yammacin Najeriya.

Wannan na ƙunshe a wata sanarwa da Sakataren gwamnatin jihar, Muhammad Mainasara Ahmad, ya fitar. Ya ce naɗin ya biyo bayan ƙarewar wa'adin shugabannin kananan hukumomin.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal.
Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal a cikin ofis Hoto: Aminu Tambuwal
Asali: UGC

Leadership ta rahoto cewa a sanarwan da ya fitar, SSG Mainasara ya ce:

"Sakamakon ƙarewar wa'adin shugabannin kanann hukumomi kamar yadda doka ta tanada karkashin kundin dokokin kananan hukumomi mai lamba 6 da aka yi wa garambawul, gwamna ya naɗa Kantomomi."

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Ayyana Kudirin Neman Tazarce a Zaben Jiharsa Da Ke Tafe 2023

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Gwamnan jihar Sakkwato ya amince da naɗa Ciyamomin riƙo wato Kantomomi a kananan hukumomi 23 gabanin a shirya zaɓen ciyamomi da kansiloli."

Jerin sunayen Kantomomin da Tambuwal ya naɗa

Legit.ng Hausa tattaro muku sunayen waɗanda gwamna Tambuwal ya naɗa Kantomomi da kuma kanana hukumomin da zasu yi aiki, su ne kamar haka:

1. Nasiru Babata- Tambuwal LGA

2. Ibrahim Muhammad Lawal- Tangaza LGA

3. Abubakar Salihu- Tureta LGA

4. Bello Abubakar Gwiwa- Wamakko LGA

5. Lawal Marafa Fakku- Kebbe LGA

6. Abdulkadir Arzika Wurno- Wurno LG

7. Garba Yakubu Tsitse- Gada LGA

8. Aliyu Shehu Illela- Illela LGA

9. Bello Wakili Bachaka- Gudu LGA

10. Haliru Abubakar Kilgori- Yabo LGA.

11. Wadata Muhammad- Binji LGA

12. Shehu Muhammad- Bodinga LGA

13. Umar Buda- Dange/Shuni LGA

14. Abdul-Wahab Yahaya- Goronyo LGA

15. Aminu A. Aya- Gwadabawa LGA

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyar PDP Ta Sanar da Sakamakon Zaben Fidda Ɗan Takarar Gwamna a Jihar Bayelsa

16. Abubakar Yusuf Dan-Ali- Isa LGA

17. Yahaya Abdullahi Gandi- Rabah LGA

18. Jafaru Hamza- Kware LGA

19. Umaru Danyaro- Sabon Birni LGA

20. Bello Muhammad Gunki- Silame LGA

21. Aliyu Dantani Shagari - Shagari LGA

22. Mustapha Shehu Sokoto - Sakkwato ta arewa LG

23. Faruku Abdulrahman Sayudi - Sakkwato ta kudu LG

Sakataren gwamnatin ya ƙara da cewa wannan naɗi zai fara aiki daga ranar 11 ga watan Afrilu, 2023, inji rahoton.

Ina Tinubu Ya Shiga? Sabbin Bayanai Sun Fito Kan Shugaban Kasa Mai Jiran Gado Bola Tinubu

A wani labarin kuma Jam'iyyar APC ta yi karin haske kan halin da shugaban ƙasa mai jiran gado, Bola Tinubu, yake ciki a ƙasar ketare

Kakakin APC na ƙasa, Felix Morka, ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba Tinubu zai dawo Najeriya ya tasa babban aikin da ke gabansa.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: PDP Ta Watsar da Gwamnoni 5, Ta Naɗa Wani Gwamna da Jigo a Babban Muƙami

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262