Ana Gobe Zabe, Jam'iyyar PDP Ta Dakatar Da Shugabanta Da Mataimakinsa a Jihar Legas

Ana Gobe Zabe, Jam'iyyar PDP Ta Dakatar Da Shugabanta Da Mataimakinsa a Jihar Legas

  • Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta ɗauki matakin ladabtar da shugaban jam'iyyar da mataimakinsa a Jihar Legas
  • Ana zargin shugabannin biyu da laifin yi wa jam'iyyar zagon ƙasa a zaɓen gwamnan da ya gabata
  • An dakatar da shugabannin biyu bisa tulin zarge-zargen cin dunduniyar jam'iyyar da ake yi mu su

Jihar Legas- Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Legas ta dakatar da shugabanta Mr. Philip Aivoji da mataimakinsa Mr. Tai Benedict, bisa zargin keta haddin kundin tsarin mulkin jam'iyyar.

Shugabannin jam'iyyar na mazaɓar E a ƙaramar hukumar Badagry da na mazaɓar J1 a ƙaramar hukumar Epe suka tabbatar da dakatar da shugabannin, cewar rahoton Vanguard

Jam'iyyar PDP ta dakatar da shugaban ta da mataimakin sa a Legas
Dumbin mutane a wajen taron PDP Hoto: PDP
Asali: UGC

Dalilin dakatar da shugaban PDP da mataimakinsa a Legas

A wata sanarwa da shugabannin jam'iyyar na mazaɓar E suka rattaɓawa hannu ranar Alhamis, sun bayyana cewa an dakatar da shugaban ne bisa cin dunduniyar ta a lokacin zaɓe.

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyar PDP Ta Sanar da Sakamakon Zaben Fidda Ɗan Takarar Gwamna a Jihar Bayelsa

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ana zargin sa da karɓar kuɗi a hannun jam'iyyar Labour Party (LP) gabanin zaɓen gwamnan jihar na ranar 18 ga watan Maris, domin sanya mambobin jam'iyyar a jihar su zaɓi jam'iyyar Labour Party.

Ana kuma zargin sa da yin sama da faɗi da kuɗaɗen da uwar jam'iyyar ta ƙasa ta turo na waɗanda suka siya fam ɗin takara a jihar. Hakan a cewar su ya saɓa wa sashi 58 (1) D na kundin tsarin mulkin jam'iyyar.

A cikin wata sanarwa makamanciyar wannan da shugabannin jam'iyyar na mazabar J1 suka fitar, sun sanar da dakatar da mataimakin shugaban jam'iyyar na jihar bayan sun yi nazari kan abubuwan da yayi a lokacin zaɓen gwamnan jihar.

Ana zargin Benedict karɓar kuɗi a hannun LP domin sanya ƴan PDP su ƙi zaɓar dan takarar jam'iyyar ta hanyar kira da tura saƙonnin waya, a cewar The street journal

Kara karanta wannan

A Watan Azumi, Tsoffin Ministoci Biyu da Wasu Jiga-Jigan PDP 2 Sun Shiga Tsaka Mai Wuya

Da shi da shugaban jam'iyyar na jihar ana kuma yi musu zargin cewa sun yi wa shugaban jam'iyyar na ƙasa ƙagen cewa shine ya ba su umurnin da su ci dunduniyar jam'iyyar.

Matasan Jam'iyyar PDP Sun Nemi a Sake Duba Kokarin Jam'iyya a Zaben 2023

A wani rahoton na daban kuma, wasu matasa a jam'iyyar PDP sun yi kiran da ayi duba kan kataɓus ɗin da jam'iyyar tayi a zaɓen 2023.

Matasan sun kuma miƙa sabbin buƙatun su ga shugaban riƙo na jam'iyyar ta PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng