Matasan Jam'iyyar PDP Sun Nemi a Sake Duba Kokarin Jam'iyya a Zaben 2023
- Ƙungiyar matasa The Young Democrats ta yi kira manyan PDP su zauna su duba abinda jam'uyyar ta taɓuka a babban zaɓen 2023
- Mai magana da yawun kunguyar matasan PDP, Alaibi Joseph, ya ce ya kamata a yi nazari kan kokarin PDP a jihohi 36 da Abuja
- Bayan haka sun buƙaci Sakataren jam'iyyar na kasa ya gaggauta yin murabus tun da ya lashe tikitin takarar gwamna a Imo
Abuja - Ƙungiyar matasa mai alaƙa ta kusa da jam'iyyar PDP, watau 'The PDP Young Democrats' ta yi kira da a gaggauta nazari kan rawar da jam'iyyar ta taka a babban zaɓen 2023.
Punch ta rahoto cewa ƙungiyar ta nemi mahukuntan PDP su yi nazari kan ƙoƙarin da jam'iyyar ta yi a faɗin jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja lokacin zaɓen da aka kammala.
Bayan haka, matasan sun bukaci shugaban PDP na riko, Umar Damagun, ya shirya taron kwamitin zaratswan PDP na ƙasa, ba tare da wani dogon turanci ba domin warware batutuwan da suka zame wa jam'iyar ƙarfen kafa.
Mai magana da yawun ƙungiyar matasan ta ƙasa, Alaibi Joseph, ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Mista Joseph ya kuma buƙaci sakataren PDP na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, wanda ya lashe tikitin takarar gwamna a jihar Imo, ya gaggauta yin murabus daga kan muƙaminsa.
Kwamitin zaɓe ya ayyana Anyanwu a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na fidda ɗan takarar gwamnan jihar Imo karkashin inuwar PDP.
Imo na ɗaya daga cikin jihohi uku da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta tsara gudanar da zaɓen gwamna ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023.
Jam'iyyar PDP ta sha kaye a hannun APC a zaben shugaban kasa, haka nan ta rasa wasu jihojin da take mulki a babban zaben da aka kammala.
APC ta gano ɗan majalisar da ke mata zagon ƙasa a Kebbi
A wani labarin kuma Jam'iyyar APC Ta Dakatar da Ɗan Majalisar Wakilan Tarayya a Jihar Kebbi
Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Kebbi ta dakatar da ɗan majalisar wakilan tarayya na mazaɓar Koko-Basse, Hon. Shehu Muhammed Koko. Matakin na zuwa ne yayin da APC ke shirin tunkarar karishen zaɓen gwamna a Kebbi ranar Asabar 11 ga watan Afrilu, 2023.
Asali: Legit.ng