Ba Sauran Zama da Zaran Tinubu Ya Dawo Gida Najeriya, APC

Ba Sauran Zama da Zaran Tinubu Ya Dawo Gida Najeriya, APC

  • Jam'iyyar APC mai mulki ta ce Bola Tinubu na nan lafiya kalau kuma nan ba da daɗewa ba zai shigo Najeriya
  • Mai magana da yawun APC ta ƙasa, Felix Morka, ya ce da zaran Tinubu ya dawo zai ci gaba da shirin karban mulki
  • A hukumance, shugaban ƙasa mai jiran gado ya bar Najeriya ranar 22 ga watan Maris zuwa nahiyar Turai domin ya samu hutu

Abuja - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta ce da zaran zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya dawo Najeriya daga Turai zai ɗora aiki daga inda ya tsaya.

Haka nan kuma Jam'iyyar ta ce shugaban ƙasa mai jiran gado, wanda ya sa kafa ya bar Najeriya tun ranar 22 ga watan Maris, zai dawo nan ba da jimawa ba gabanin ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

Kara karanta wannan

Suna Dab Da Barin Mulki, Hadimin Shugaba Buhari Ya Yi Wa Shahararren Malamin Addini Kaca-Kaca

Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban ƙasa mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bola Tinubu
Asali: UGC

Sakataren yaɗa labarai na APC ta ƙasa, Felix Morka ne ya yi wannan furucin a cikin shirin Politics Today na Channels tv ranar Alhamis, 13 ga watan Afrilu, 2023.

Yayin da aka tambaye shi ko ina zaɓabben shugaban ƙasan ya shiga yanzu haka, Kakakin APC ya bayyana cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Yana nan lafiya kalau, bayan kammala zaɓe da duk faɗi tashin da aka yi na gajiya, ya yanke shawarin ya ɗan tafi ya sarara, ya samu hutu."
"Da zaran ya dawo gida Najeriya kuma aka rantsar da shi ranar 29 ga watan Mayu, 2023, babu sauran zama, nauye-nauye zasu hau kansa na jan ragamar ƙasa mai girma kuma mai ɓangarori kamar Najeriya."
"Na san cewa nan ba da jimawa ba (shugaban ƙasa mai jiram gado) zai dawo gida Najeriya."

Meyasa Tinubu ya tafi ƙasar ƙetare?

Kara karanta wannan

Gwamna Wike Ya Kara Yi Wa Ayu Shaguɓe, Ya Kama Hanyar Hargitsa PDP Bayan Zaben 2023

Mista Morka ya ƙara da bayanin cewa tsohon gwamnan Legas ɗin ba zai samu hutu yanda ya dace ba idan ya zauna a Najeriya bayan zaɓe, mutane zasu dame shi don neman muƙami.

Kakakin APC ya ce duk waɗanda ya zama wajibi suna gana wa da Tinubu ta fasahar zamani ko fuska da fuska kuma ya kamata kowa ya sani yana aiki kan abinda ke tunkarowa.

Atiku Ya Ja Hankalin Mutane Su Zabi PDP a Adamwa da Kebbi

A wani labarin kuma Kwana ɗaya gabanin karisa zaben gwamna a Adamawa da Kebbi, Atiku ya yi magana kan yan takarar da yake goyon baya

Tsohon mataimakin shugaban kasan ya roki masu kaɗa kuri'a a jihohin Adamawa da Kebbi, su taimaka su zabi jam'iyyar PDP a gobe Asabar.

Bayan ayyana zaɓe a matsayin wanda bai kammalu ba, INEC ta shirya karisa zabe a jihohin da abun ya shafa ranar 15 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban Kasa Ta Bayyana Namijin Kokarin da Buhari Ya Yi Na Dawo da Zaman Lafiya a Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262