Zababben ‘Dan Majalisar Kano a Jam’iyyar NNPP Ya Rasa Kujerarsa a Gwamnatin Buhari
- Abdulmumin Jibrin ya tashi daga matsayin Darekta a Hukumar FHA mai kula da gidajen tarayya
- An kafa wani kwamiti a FHA wanda ya yi bincike a kan ‘dan siyasar, sai aka same shi da aikata laifi
- Hon. Jibrin ya daina zuwa ofis ba tare da wani dalili ba, zababben ‘dan majalisar ya ce ya yi murabus
Abuja - Majalisar da ke kula da aikin Hukumar gidaje ta FHA, ta kori Abdulmumin Jibrin bayan samun shi da aikata mummunan laifi a bakin aiki.
Rahoton da aka samu a Daily Trust ya ce Hon. Abdulmumin Jibrin ya bar kujerar da yake kai ta Darektan bincike da dabaru da kawo cigaba a FHA.
Wasikar da Sakataren majalisar, Alhaji Aliyu Jafaru Laura ya fitar a ranar 6 ga watan Afrilu ta nuna ana zargin Jibrin da watsi da wajen aikin na sa.
Ganin ya yi wata da watanni bai je ofis ba, aka kafa wani kwamitin ladabtarwa wanda a karshen zaman da ya yi, ya bada shawarar a sallami Darektan.
Shiga takara yana kan kujera
Kwamitin da aka kafa ya gano cewa ‘dan siyasar ya shiga takarar ‘dan majalisar wakilan tarayya a Kiru/Bebeji, ba tare da ya yi murabus daga FHA ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Tsohon ‘dan majalisar zai sake wakiltar mazabarsa ta Kano bayan nasarar da ya samu a jam’iyyar hamayya ta NNPP a zaben da aka yi a watan Fubrairu.
Ana sauraron martanin Hon. Jibrin
Rahoton yake cewa Hon. Jibrin ya yi watsi da maganar korarsa daga aikin, ya ce zancen banza ne.
Da aka tuntubi zababben ‘dan majalisar, ya shaida cewa ya dade da yin murabus, ya kuma yi alkawarin zai nunawa ‘yan jarida hujjojin da ke nuna haka.
"Tuni na yi murabus daga mukamin. Ko ma ya abin yake, ba su da ikon da za su yi haka (kore ni). Amma ku ba ni ‘yan sa’o’i in aiko maku da martani na."
- Abdulmumin Jibrin
Takardar sallamar FHA ta zargi tsohon Darektan da sabawa dokokin aikin gwamnati, ta ce an kuma saba sassan 8.1.2(b) da 8.1.7 na tsarin aikin hukumar.
Binciken da kwamiti ya gudanar
Shugaban kwamitin da ya jagoranci binciken da aka yi, Barista Zubairu Suleiman ya ce an yi ta aika wanda aka sallamar takarda domin ya iya kare kan shi.
Suleiman yake cewa ‘dan siyasar ya kauracewa aikinsa ba tare da kwakkwaran dalili ba.
Zaben majalisar tarayya
Francis Waive ya aikawa ‘Yan majalisa sako ta manhajar WhatsApp, ya fada masu cewa zai nemi takarar mataimakin shugaban majalisar wakilan tarayya.
‘Dan siyasar zai nemi takarar ne da sharadi daya, a kebewa yankin Kudu maso kudu kujerar, idan aka yi haka, zai mika kansa domin ya hidima a majalisa.
Asali: Legit.ng