Fafutukar Shugabancin Kasa: Atiku, Obi Da Sauran Masu Son Ganin An Tsige Tinubu
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) shine ya lashe zaben ranar 25 ga watan Fabarairu.
A cewar hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC), Tinubu ya samu kuri'u miliyan 8.8 wajen yin nasara.
Sai dai kuma, biyar daga cikin abokan hamayyarsa suna kalubalantar sakamakon zaben a kotu.
1. Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin Shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya kasance dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Shi ya zo na biyu da kuri’u 6,984,520.
Duk cewar shi ya zo na biyu, jigon na PDP ya shigar da kara gaban kotun zaben shugaban kasa inda ya nemi a ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.
2. Peter Obi
Peter Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra ya yi takara karkashin inuwar jam’iyyar Labour Party kuma shi ya zo na uku da kuri’u 6,101,533.
Sai dai kuma, Obi ya yi ikirarin cewa shine ya lashe zaben kuma zai tabbatar da hakan a kotu.
3. Action Peoples Party (APP)
Jam’iyyar Action Peoples Party (APP) ta bukaci kotu ta soke nasarar Tinubu yayin da ta zargi zababben Shugaban kasar da magudi a zaben 25 ga watan Fabrairu.
Legit.ng ta tattaro cewa dan takarar shugaban kasa na APP a zaben, Nnadi Osita ya samu kuri’u 12,839.
4. All Peoples Movement (APM)
Jam’iyyar All Peoples Movement (APM) itama ta bukaci kotun zabe ta tsige zababben shugaban kasa Tinubu.
Jam’iyyar ta yi ikirarin cewa nasarar dan takarar shugaban kasar na APC ba zai yi tasiri ba saboda tsarin da aka keta wajen zabar mataimakinsa, Kashim Shettima.
5. Action Alliance (AA)
Jam’iyyar Action Alliance (AA) na so kotu ta soke zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu saboda INEC ta ki saka sunan ainahin dan takararta na shugaban kasa - Solomon-David Okanigbuan- a shafinta.
Jam’iyyar ta ce duk da umurnin kotu da ta shaida Okanigbuan a matsayin sahihin dan takararta, INEC ta saka sunan Hamza Al-Mustapha.
Sau 19 Wike ya kirani yana so ya zama mataimakin Atiku, Dino Melaye
A wani labari na daban, Sanata Dino Melaye ya bayyana cewa sau 19 gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya kira shi yana neman ya tsaya masa don ya zama abokin takarar Atiku Abubakar a zaben 2023.
Asali: Legit.ng