Jerin Sanatocin Arewa Da Ke Neman Kujerar Shugaban Majalisar Dattawa
A ranar 29 ga watan Mayu, 2023, wa'adin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, yake ƙarewa kuma a wannan rana za'a rantsar da sabon shugaban kasa, Bola Tinubu.
Yayin da shugaban ƙasa mai jiran gado ke shirye-shiryen ɗarewa kan madafun iko, Zaɓaɓɓun Sanatoci da mambobin majalisar wakilar na yunkurin samun shugabanci a majalisa ta 10.
Zuwa yanzun an samu sanatoci daga kudu da arewacin Najeriya da suka nuna sha'awar neman kujerar shugaban majalisar dattawa, kamar yadda Pulse ta rahoto.
A wannan babin, Legit.ng Hausa ta tattaro muku jerin Sanatocin da suka fito daga arewacin Najeriya, wanda suka shiga tseren gaje kujerar Sanata Ahmad Lawan a majalisar dattawa.
1. Sanata Barau Jibrin
Sanata Jibrin Barau, mai wakiltar mazaɓar Kano ta arewa a majalisar Dattawa, karo na huɗu kenan da Barau Jibrin zai shiga majalisar tarayya a tarihin siyasarsa.
Ana Saura Awanni 24: Atiku Ya Yi Magana Mai Jan Hankali Game da Cikon Zaɓen Gwamna a Adamawa da Kebbi
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yanzu haka shi ne shugaban kwamitin kasafin kuɗi. Baya ga sha'awar da ya nuna kan babbar kujerar majalisar dattawa, wasu jiga-jigan APC sun fara tama shi kamfen gaje Lawan a majalisa ta 10.
Sun bayyana cewa tun da shugaban kasa da mataimakinsa sun fito daga kudu maso yamma da arewa maso gabas, kamata ya yi a baiwa arewa ta yamma shugaban majalisar dattawa.
2. Abdul'aziz Yari
Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdul'aziz Yari, ya shiga tseren kujerar shugaban Majalisar dattawa. Ya ayyana kudirinsa a watan Maris, 2023.
Yari ya yi musun cewa shiyyar arewa maso yamma ce ta baiwa jam'iyyar APC kuri'u mafi rinjaye a zaɓen shugaban kasan da ya gudana ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.
Tsohon gwamnan zai wakilci al'umma mazaɓar Zamfara ta yamma a majalisa ta 10.
3. Sanata Ahmad Lawan
Shugaban majalisar dattawa na yanzu a majalisar tarayya ta 9, Sanata Ahmad Lawan, a karo na biyu ya sake shiga tseren kujerar a majalisa ta 10.
Lawan, mai wakiltar Yobe ta arewa na ɗaya daga cikin yan majalisun da suka jima tun shekarar 2007. Shi ne ya gaji Bukola Saraki a 2019 kuma yana burin ci gaba da zama har zuwa 2027.
4. Sanata Sani Musa
Sanata Sani Musa, mai wakiltar mazaɓar Neja ta gabas na cikin jiga-jigan APC da ke sha'awar ɗarewa kujerar shugaban majalisar dattawa.
Punch ta rahoto cewa Sanatan na samun goyon baya daga ƙungiyoyin magoya bayan jam'iyya mai mulki, wanda a cewarsu yana da gogewar zama shugaban majalisar dattawa ta 10.
5. Sanata Ali Ndume
Sanata Ali Ndume, na mazaɓar Borno ta kudu a arewa maso gabashin Najeriya ya shiga tseren gaje Ahmad Lawan a majalisa ta 10.
Ndume ya yi zargin cewa masu fafutukar neman mulkin majalisar dattawa sun fara kokarin sayen goyon baya da kuɗi don cimma burinsu.
A wani labarin kuma Shugaban Masu Rinjaye Na Majalisar Dokokin Jihar Kogi Ya Yi Murabus Kan Bakin Fentin da aka shafa masa
Biyo bayan zargin gwamna Yahaya Bello ya yi wa yan majalisu 9, shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin Kogi ya sauka daga muƙaminsa.
Sai dai bayan karanta wasikar murabus dinsa, nan take mambobin majalisar suka zaɓi sabon shugaban masu rinjaye wanda zai maye gurbinsa.
Asali: Legit.ng