“Sau 19 Wike Ya Kirani Yana Kamun Kafa Don Zama Abokin Takarar Atiku” - Dino Melaye

“Sau 19 Wike Ya Kirani Yana Kamun Kafa Don Zama Abokin Takarar Atiku” - Dino Melaye

  • Rikicin da ya dabaibaye babbar jam’iyyar adawar kasar ya dauki sabon salo yayin da Gwamna Nyesom Wike da Dino Melaye suka yi kaca-kaca
  • Rikicin PDP ya kara kamari yayin da Melaye ya bayyana yadda Wike, gwamnan jihar Ribas ya roke shi sau 19 don ya zama abokin takarar Atiku Abubakar
  • Da yake kara fallasa sirrin Wike, Melaye, mai neman takarar gwamnan jihar Kogi ya ce yana da bidiyon kiransa da ya yi a matsayin hujja

Rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) bai da ranar karewa da sabon fallasar da tsohon sanatan Kogi, Dino Melaye ya yi game da kamun kafa da Gwamna Nyesom Wike ya dungi yi don samun mukamin mataimakin shugaban kasa.

Dino Melaye, ya ce gwamnan na jihar Ribas na ta kamun kafa don zama abokin takarar Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 25 ga watan Fabrairu, jaridar The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Gwamna Gandije ya caba, majalisa ta amince da kudurinsa kan masarautun Kano

Nyesom Wike da Dino Melaye
“Sau 19 Wike Ya Kirani Yana Kamun Kafa Don Zama Abokin Takarar Atiku” - Dino Melaye Hoto: Gov Nyesom Ezenwo Wike - CON, Dino Melaye
Asali: Facebook

Yadda Wike ya roke ni don zama mataimakin Atiku, Melaye ya magantu

Da yake jawabi a wata hira da Arise TV a ranar Laraba, 12 ga watan Afrilu, Melaye ya yi ikirarin cewa Wike ya kira shi sau 19 don ya zama abokin takarar Atiku.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Melaye ya kara da cewar adawar da Wike ke yi da shi ya kasance saboda ya ki marawa kudirinsa na son zama shugaban kasa baya.

Ina da bidiyo, Dino ya bayyana

Dino Melaye ya ce gwamnan na Ribas yana fada da Atiku ne saboda ya zabi Gwamna Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takararsa bayan shi ya yi zawarcin wannan kujera bai samu ba, Nigerian Tribune ta rahoto.

Wike ya marawa kudirina na neman gwamna a 2019 baya, Inji Melaye

Melaye ya ci gaba da bayyana cewa Wike shine babban wanda ya dauki nauyin abun lokacin da ya nemi takarar wannan kujera a 2019.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnan Kogi: Dino Melaye Ya Mayarwa Wike Da Zazzafan Martani, Ya Ce Ya San Abun da Ke Yi Masa Ciwo

Ya ce:

“Wike ya kasance babban magoyin bayana; ya kasance babban masoyina da ya kai daruruwan dubban dala. Ba iya zaben fidda gwanina ya marawa baya ba, ya samar da jirgin sama mai zaman kansa da zai ajiyeni a Kogi a ranar zaben fidda gwani sannan ya kirani akai-akai bayan nan.
“Wike baida digon mutunci. Wike na ta kirana lokacin da Atiku Abubakar zai sanar da abokin takararsa. Ina da faifan kuma zan fitar da su. Ina jiransa.”

Dino bai cancanci zama gwamnan jihar Kogi ba, Wike

A gefe guda, Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya ce Sanata Dino Melaye bai da abun da ake bukata don zama gwamnan jihar Kogi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng