Shugaban Masu Rinjaye Na Majalisar Dokokin Jihar Kogi Ya Yi Murabus
- Rikicin da ya biyo bayan zaben 18 ga watan Maris, ya jawo shugaban masu rinjaye na majalisar jihar Kogi ya yi murabus
- Gwamna Yajaya Bello ne ya shafa mai fentin zargin hannu a ta'addanci ranar zaben, tare da wasu mambobi
- Tuni majalisar ta amince da naɗa Ahmed Ɗahiru a matsayin wanda zai maye gurbin shugaban masu rinjaye
Kogi - Shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Kogi, Alhaji Murktar Bajeh (APC-Okehi), ya yi murabus daga kan muƙaminsa.
Honorabul Bajeh, mai wakiltar Okehi a inuwar APC, ya ɗauki wannan matakin ne domin nuna adawa da zargin ta'addancin da aka ɗora masa tare da abokan aikinsa 8.
Wa ya ɗora musu zargin aikata ta'addanci?
Gwamnan Kogi, Yahaya Bello, a ranar 25 ga watan Maris, ya shafa wa mambobi 9 cikin 25 na majalisar dokokin fentin 'yan ta'adda saboda abinda ake zargin sun aikata ranar zaɓe 18 ga watan Maris.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Daily Trust ta rahoto cewa a wata wasiƙa da ya aike wa kakakin majalisar, Matthew Kolawale, Bello ya buƙaci a dakatar da 'yan majalisun guda tara ciki harda shugaban masu rinjaye.
Bugu da ƙari, gwamna Yahaya Bello, ya roki majalisar ta gudanar da bincike don tabbatar da rawar da suka taka ranar zaben 'yan majalisun jiha watau 18 ga watan Maris.
Ya miƙa takardar murabus
Amma Bajeh, a wata takarda da ya tura wa majalisar, ya sanar da shawarin da ya yanke na sauka daga muƙamin shugaban masu rinjaye, kamar yadda The Nation ta ruwiato.
Kakakin majalisar ya nemi mambobi su faɗi ra'ayoyinsu kan murabus ɗin shugaban masu rinjaye bayan karanta takardarsa a zauren majalisa.
Nan take mataimakin kakaki, Alfa Momoh-Rabiu, ya ba da shawarin naɗa Mai ladabtarwa, Ahmed Dahiru, ya maye gurbin Bajeh a matsayin shugaban masu rinjaye.
Majalisa ta naɗa sabon shugaban masu rinjaye
Cikin hanzari shugaban majalisar ya jefa tambaya ga sauran mambobi, su amince ko akasin haka game da shawarin naɗa Mai ladabtarwa a matsayin sabon shugaban masu rinjaye.
Nan take mambobin majalisar suka amince da Honorabul Ahmed Dahiru a matsayin sabon shugaban masu rinjaye.
A wani labarin kuma Gwamna Douye Diri Ya Lashe Tikitin Neman Tazarce a Zaben Gwamnan Bayelsa
A ranar Laraba PDP ta gudanar da zaɓen fidda gwani kuma Gwamna Diri ya lashe ba tare ɗa hamayya ba.
Ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023, INEC zata gudanar da zaɓen gwamna a jihar Bayelsa da kuma jihohin Imo da Kogi.
Asali: Legit.ng