PDP Zata Hukunta Tsoffin Ministoci da Wasu Jiga-Jigai 2 Bisa Goyon Bayan APC
- Jam'iyyar PDP ta fara shirin hukunta tsoffin ministoci biyu da wasu jiga-jiganta biyu a jihar Kebbi
- A wata wasiƙar tuhuma da ta aike wa mutanen ta nemi su kare kansu kan zargin zagon ƙasa cikin awanni 48
- Ana zargin tsoffin Ministocin da goyon bayan ɗan takarar gwamnan APC a zaben 18 ga watan Maris, 2023
Kebbi - Jam'iyyar adawa watau PDP reshen jihar Kebbi ta hannun gundumar Ɗangaladima, ranar Laraba, ta tuhumi tsohon minista, Buhari Bala, ya kare kansa kan zargin cin amana.
Shugaban PDP na gundumar Ɗangaladima, Alhaji Umaru Dattiya, ya ce sun ɗauki wannan matakin na neman karin haske daga bakinsa bayan gudanar da bincike mai zurfi kan yadda yake tafiyar da al'amuransa.
A cewarsa, ana zargin Bala ya goyi bayan ɗan takarar gwamnan jam'iyyar APC ta bayan fage a zaɓen ranar 18 ga watan Maris, 2023, maimakon ɗan takarar PDP a Kebbi.
Umaru Dattiya ya ƙara da cewa tsohon ministan ya daina biyan kuɗin haraji ga jam'iyyar PDP, kuma bincike ya nuna akwai ayar tambaya a harkokinsa, inji rahoton Vanguard.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Bugu da ƙari, ya ce sun samu rahoton da ke nuna cewa ya shirye dabaru da manaƙisa, harda bayar da makudan kuɗaɗe domin tabbatar da APC ta samu nasara ranar zaɓe.
Takardar tuhumar ta samu sa hannun shugabanni 17 na gundumar Ɗangaladima ciki harda shugaba, Umaru Dattiya da Sakatarensa, Sirajo Ibrahim. Sun baiwa jigon awanni 48 ya kare kansa.
Wani minista da mutum 2 sun shiga matsala
Haka zalika, shugabanni 12 a gundumar Nasarawa 1 da ke yankin Birnin Kebbi sun nemi karin haske daga tsohon ministan ayyuka na musamman, Kabiru Tanimu Turaki.
Sun kuma ba shi wa'adin awanni 48 ya maida martani kan zargin da ake masa da wasu mutum biyu da aikata zagon ƙasa ga PDP lokacin zaben gwamnan jihar Kebbi.
Legit.ng Hausa ta gano cewa Tanimu, General Sarkin Yaki Bello da kuma Haruna Dan Dio, su ne mutane uku da tuhumar ta shafa.
Kotu Ta Rushe Sabon Kwamitin Shugabannin PDP Na Riƙo a Jihar Katsina
A wani labarin kuma Babbar Kotu Ta Kara Hargitsa PDP, Ta Kori Shugabannin Jam'iyya a Jihar Katsina
Jam'iyyar PDP ta sake shiga ruɗani a kokarinta na ɗinke barakar da ta kunno a jihar Katsina.
Babbar Kotu ta tsige kwamitin rikon kwaryan da PDP ta naɗa kwanan nan a jihar, ta ce a jira ta gama zaman sauraron korafin da aka kai mata.
Asali: Legit.ng