2023: "Ba Abinda Zai Iya Kawo Mana," Gwamna Wike Ya Ƙara Yi Wa Ayu Shagube

2023: "Ba Abinda Zai Iya Kawo Mana," Gwamna Wike Ya Ƙara Yi Wa Ayu Shagube

  • Gwamna Nyesom Wike ya ƙara yi wa tsohon shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Dr Iyorchia Ayu, shaguɓe kan rashin nasara a 2023
  • Wike, jagoran masu fafutukar dole Ayu ya yi murabus gabanin zaɓe, ya ce ta tabbata Ayu ba zai iya tsinanawa PDP komai ba
  • Tuni dai jam'iyyar PDP ta sauya Ayu bayan umarnin Kotu a jihar Benuwai, ta maye gurbinsa da mataimakinsa na shiyyar arewa

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya sake yi wa tsohon shugaban PDP na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu, shaguɓe kan kashin da jam'iyyar ta sha a zaɓen shugaban kasa na 2023.

Wike, wanda ya jagoranci kiraye kirayen Ayu ya yi murabus a kakar babban zabe, ya ce haifaffen jihar Benuwai, Ayu, ba shi da basira ko ƙima a zaɓe, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

Kara karanta wannan

"Mu Tari 2027" Sanatan APC Ya Yi Magana Kan Sahihancin Zaben 2023, Ya Aike da Sako Ga Atiku da Obi

Gwamna Wike da Ayu.
Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike da tsohon shugaban PDP, Iyorchia Ayu Hoto: Nyesom Wike
Asali: Facebook

A wata hira da ya yi da 'yan jaridan da aka zaɓa a Patakwal, babban birnin jihar Ribas ranar Talata, gwamna Wike ya ce:

"Yanzu kun gani da idonku cewa ba abinda zai iya kawo wa jam'iyya. Mun ci zaɓe a nan (Ribas) wanda ke nuna zamu iya kawo wa jam'iyya wani abu, Ayu ba zai iya tsinana komai ba."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Game da matakin PDP na naɗa shugaban jam'iyya na rikon kwarya, gwamna Wike ya ce ci gaban ya ɗan yi amfani amma ya nuna farin cikin cewa Ayu bai bar shugabanci ba sai bayan zaɓe.

"Menene amfanin Ayu ya kauce gefe guda (daga kujerar shugaban PDP na ƙasa)?" Gwamnan Ribas ya tambaya.

Amma ya kara da cewa, "Mun ji daɗi sosai kasancewar Ayu bai sauka ba a wancan lokacin sabida da ace ya tafi, za su fito su ce ai saboda ya sauka ne shiyasa muka yi rashin nasara."

Kara karanta wannan

Gwamna El-Rufai Ya Yaba Wa Wike, Ya Faɗi Tarihin da Mutanen Ribas Suka Kafa a Siyasar Najeriya

PDP Ta Jingine Wike, Makinde da Wasu Gwamnoni, Ta Naɗa Adeleke a Babban Muƙami

A wani labarin kuma PDP Ta Watsar da Gwamnoni 5, Ta Naɗa Wani Gwamna da Jigo a Babban Muƙami

Har yanzun ana takun saƙa tsakanin gwamnonin G-5 da uwar jam'iyyar PDP ta ƙasa bayan abinda ya faru a zaben shugaban ƙasan 2023.

Rigimar ta kara hitowa fili ne bayan PDP ta sanar da shugabannin kwamitocin shirya zaben fidda ɗan takarar gwamna a jihohi 2.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262