Gwamnoni Sun Hango Matsala a Majalisa, Sun Nemi a Dauki Matakin Gaggawa a APC
- Ana tunanin Gwamnoni Jam’iyyar APC za su hadu da ‘Yan majalisar NWC da Bola Tinubu
- Makasudin zaman shi ne a san daga inda za a fito da ‘yan takarar shugaban majalisar tarayya
- Lokaci ya na ta tafiya, APC ba ta iya tsaida magana a kan yadda za a ware kujerun majalisa ba
Abuja - Gwamnonin da ke mulki a karkashin APC sun yi kira ga jam’iyya mai mulki tayi maza ta tsaida yankin da za a kai shugabancin majalisa.
Rahoton The Nation ya nuna Gwamnonin jihohi su na so jam’iyyar APC ta tsaida magana kan daga ina za a fito da shugabannin majalisar tarayya.
Har yanzu APC ba ta fadi yankin da aka kebewa takarar shugaban majalisar dattawa da na wakilai ba, wannan ya sa masu harin mukami suka taru.
Wata majiya ta ce Gwamnonin APC sun kira taro da shugabannin majalisar gudanarwa da APC watau NWC kan maganar takarar ‘yan majalisa.
Gwamnoni za su kuma zama
Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu yana cikin wadanda aka gayyata zuwa wajen taro domin a yanke shawara yankin kasar da za a warewa takara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A makon da ya gabata, Gwamnonin suka yi taro a Birnin tarayya Abuja, su ka tattauna a kan wasu daga cikin masu neman shugabancin majalisa.
Wasu da ke kusa da Gwamnonin sun nuna ana la’akari da sha’anin addini wajen zakulo wadanda za su gaji Ahmad Lawan da Femi Gbajabiamila.
Ganin Bola Tinubu da Kashim Shettima sun fito daga yanki daya da Gbajabiamila da Lawan, da kamar wahala su iya cigaba da zama a kan kujerunsu.
Kudu maso Kudu da Arewa maso tsakiya
Da alama matsayar Gwamnonin ita ce shugaban majalisar dattawa ya zama ‘Dan Kudu maso kudu, hakan yana nufin zai zama Kirista daga APC.
Rahoton ya ce akwai yiwuwar wanda zai zama sabon shugaban majalisar wakilan tarayya a watan Yuni ya fito daga shiyyar Arewa maso tsakiya.
Idan an zauna da shugabannin APC da shugaban kasa mai jiran-gado, babu mamaki a canza shawara, hakan ya jawo lissafin gwamnonin ya canza.
Su wanene ke takara a 2023?
An ji labari Ahmad Lawan, Godswill Akpabio, Barau Jibrin, Ali Ndume su na takara. Haka zalika Sani Musa, Orji Kalu, Osita Izunaso da Dave Umahi.
Idris Wase, Yusuf Gagdi, Abdulraheem Olawuyi, Aliyu Mukthar Betara, Benjamin Kalu, Tajudeen Abbas, Sada Soli su na takara a majalisar wakilai.
Ragowar masu neman zama shugaban majalisar su ne Abubakar Makki Yalleman da Aminu Jaji.
Asali: Legit.ng